Kano: Matasa 2 Da Suka Ci Kwalan Limamin Unguwarsu A Masallaci Sun Gamu Da Fushin Kotun Musulunci

Kano: Matasa 2 Da Suka Ci Kwalan Limamin Unguwarsu A Masallaci Sun Gamu Da Fushin Kotun Musulunci

  • Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta gurfanar da mutane biyu bisa zargin cin zarafin limamin masallacin unguwansu
  • Mutanen biyu, Ada da Muslim sun ci zarafin limamin ne bayan da suka shake masa wuyar riga da jawo shi wajen masallacin
  • Matasan sun musanta aikata wannan mummunan laifin, yayin da alkalin kotun bai yi wata wata ba ya tura su gidan kaso

Jihar Kano - Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a PRP Gama cikin jihar Kano ta garkame mutane biyu bisa zargin cin zarafin wani limamin masallaci a cikin unguwar.

Wandanda ake zargin, Ada Yahaya da Muslim Ibrahim sunyi kokarin dukan limamin ne mai suna Mallam Muhammada Auwal Tsamiya wanda shine ya ke jan sallah a masallacinsa da ke Hotoro a cikin kwaryar Kano.

sharia
Kotun shari'a, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Mutanen biyu wadanda ake zargin, an tusa keyarsu ne zuwa kotu wanda Nura Yusuf Ahmad ke jagoranta kuma ana zarginsu ne da laifuka 3 da suka hada da cin zarafi da nuna karfi da kuma hadin baki.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutanen biyu sun shake wuyan rigar limamin kuma suka jawo shi waje saboda basa sonshi a matsayin limamin masallacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun musanta zargin da ake musu

Bayan karanto musu laifukansu, wadanda ake zargin, Ada da Muslim sun musanta aikata wannan mummunan laifin.

Alkalin kotun ya bada umarnin tsaresu a gidan gyaran hali kuma ya daga sauraron karar zuwa wani lokaci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matasan bayan sun musanta zargin da ake musu, ba su nuna wani damuwa ko dana sani ba game da abinda ya faru, tuni aka tisa keyarsu zuwa gidan gyaran hali zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.

Hisbah a Kano Ta Gargadi Masu Adaidaita Sahu Kan Manna Hotunan Badala

Hisbah a jihar Kano ta gargadi matasa a jihar musamman yadda masu adaidaita sahu a jihar ke manna hotunan batsa ko wasu abubuwa da ke bata tarbiyyar al’umma wanda ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.

Kwamandan hukumar Sheikh Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ga ‘yan jaridu a ofishinsa, inda ya gargadi masu adaidaita sahun da su kaucewa duk wani abu da zai gurbata tarbiyya, da jawo tashin hankali a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel