Naka Sai Naka: Jami’a, Makarantu da Sauran Jerin Manyan Ayyukan da Shugaba Buhari Ya Kai Daura

Naka Sai Naka: Jami’a, Makarantu da Sauran Jerin Manyan Ayyukan da Shugaba Buhari Ya Kai Daura

 • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina, bayan sauka daga mulki, inda ya samu kyakkyawar tarba daga mazauna garin
 • Daura ta sha fuskantar kalubale da dama kamar rashin ababen more rayuwa da gine-ginen ci gaba kafin mulkin Buhari amma garin a yanzu ya samu ci gaba sosai saboda mulkinsa
 • An samar da ayyuka da suka hada da cibiyoyin ilimi, asibitoci, layin dogo, da inganta ababen more rayuwa iri-iri

Daura, jihar Katsina - A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma mahaifarsa Daura ta jihar Katsina bayan ya mika wa magajinsa Bola Tinubu mulki a filin Eagle Square.

Yayin da ‘yan Najeriya ke ta mayar da martani daban-daban dangane da mulkinsa na shekaru takwas, ga dukkan alamu mazauna Daura sun gamsu da aikin dansu Buhari ya kai dari bisa dari.

Kara karanta wannan

Ya samu raguwar arziki: Buhari ya gama mulki, ya fadi adadin dukiyar da ya mallaka yanzu

Daga cikin abubuwan da suka faru a dawowar Buhari Daura, an shirya gagarumin bikin Durbar na musamman domin tarbar tsohon shugaban kasar zuwa gidansa.

Ayyukan da Buhari ya yiwa garinsu Daura
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Me kuka sani game da Daura, mahaifar Buhari?

Daura, karamar hukumar Katsina, gari ne mai yawan jama’a, mai dimbin tarihi tun shekaru da dama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta samar da fitattun mutane irinsu Bayajidda da Sani Zangon Daura, wadanda suka yi suna ba kawai a Najeriya ba, har ma a fadin nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Duk da haka, garin bai da wasu muhimman ababen more rayuwa kamar wuraren kiwon lafiya, ilimi, da ababen more rayuwa, wanda hakan ya sa mazauna garin fuskantar kalubale masu yawa.

Yadda Daura take a baya

Kafin mulkin shugaba Buhari, Daura ba ta da jami’a ga kuma takaitattun wuraren kula da lafiya, wanda hakan ya sa majinyata ke neman magani a wasu wuraren daban, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bidiyon Buhari Yana Mike Kafa a Gidansa Na Daura Ya Bayyana, Mutane Sun Yi Martani

Rashin isassun hanyoyin mota da makarantu masu inganci ya kuma tilastawa dimbin attajirai yin kaura zuwa garuruwan da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar don samun ingantacciyar rayuwa.

Daura bayan mulkin Buhari

Idan aka yi la’akari da ayyukan samar da ababen more rayuwa da aka gina a garin a cikin shekaru takwas da suka wuce, za a iya fahimtar dalilin da ya sa aka yi wa tsohon shugaban kasa Buhari kyakkyawar tarba.

A kasa mun kawo muku jerin wasu manyan ayyuka (da yawa an kamala su, wasu kuma ana ci gaba da yinsu) da Daura ya ci gajiyarsu a mulkin Buhai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 • Jami’ar Muhammadu Buhari ta ilimin Sufuri
 • Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Daura
 • Asibitin Sojojin Sama
 • Asibitin Mata da Yara
 • Layin dogo daga Kano zuwa Maradi (wanda ya ratsa cikin Daura)
 • Makarantar Nakasassu da masu Bukata ta Musamman
 • Sashen Sojin Saman Najeriya
 • Ajiye Sojojin Najeriya Bataliya ta 171
 • Cibiyar haihuwa mai gadaje 50 a babban asibitin Daura
 • Inganta Babban Asibitin Daura zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya
 • Ayyuka da dama na gyara, faɗaɗawa, sake farfadowa da kuma kammala ayyukan da aka yi watsi da su da kuma wadanda ake da su, wadanda suka hada da hanyoyi, makarantu, magudanar ruwa, ayyukan ruwan sha da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Mazauna Garin Daura Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Tsohon Shugaban Kasa Kura-Kuransa

Shanun Buhari sun ragu saboda yawan ba mutane da yake

A bangare guda, lissafi ya nuna cewa, shanun tsohon shugaban kasa Buhari sun ragu saboda tsananin kyauta da yake yi.

Wannan na zuwa a rahoton da ya bayar na adadin kadarorin da ya mallaka bayan kammala mulkin Najeriya shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel