Mazauna Garin Daura Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Tsohon Shugaban Kasa Kura-Kuransa

Mazauna Garin Daura Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Tsohon Shugaban Kasa Kura-Kuransa

  • Mutanen garin Daura da ke jihar Katsina sun roki ‘yan Najeriya da su yafewa tsohon shugaban kasa Buhari
  • Wasu daga cikin mazauna Daura, Lawal Ado da Umaru Yusuf ne suka yi wannan roko bayan Buhari ya isa Daura
  • Buhari ya mika mulki ne ga sabon shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a birnin Abuja

Katsina – Mazauna garin Daura da ke jihar Katsina sun roki ‘yan Najeriya su yafe wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bisa laifukan da ya aikata musu yayin mulkinsa.

Buhari ya mika mulki ne ga Shugaba Tinubu a ranar Litinin 29 ga watan Mayu bayan shafe shekaru takwas ya na mulki.

Tsohon Shugaban Kasa Buhari a Daura
Mazauna Garin Daura Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Buhari, Hoto: Channels TV.
Asali: Facebook

Buhari wanda shi kansa ya nemi afuwan ‘yan Najeriya ya koma gida Daura bayan ya mika mulki ga Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

A ranar Talata 30 ga watan Mayu, mutanen Daura, mahaifar tsohon shugaban kasa Buhari sun roki yafiya ga shugaban a wurin ‘yan Najeriya bayan sarkin Daura, Mai Martaba Umar Umar ya shirya hawan Daba domin tarbar Bayajidda II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen Daura sun nemi a yafe wa Buhari laifukansa

Rahotanni sun bayyana yadda wasu daga cikin ‘yan Dauran; Lawal Ado da Umaru Yusuf suka nuna farin cikinsu da dawowar Buhari gida a wata zantawa da gidan talabijin na Channels.

Mulkin Najeriya ba karamin abu ba ne

A cewar Lawal:

“Muna murnar dawowar shi, kun san mulkin Najeriya ba karamin abu ba ne, duk wanda ya mulki kasar har shekaru takwas kuma ya dawo lafiya, dole a godewa Allah.
“Abin da yasa muka shirya wannan hawan Daba shi ne don mu nuna masa muna tare da shi dari bisa dari, shi dan Adam ne ba zai iya gama komai ba, muna rokon ‘yan Najeriya da su yafe masa idan ya saba musu ta wasu hanyoyi."

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Kalli Bidiyon Lokacin Da Buhari Ya Tashi Zuwa Mahaifarsa Daura Bayan Mika Mulki Ga Tinubu

A cewar Umaru:

“Mu na murnar karbar 'dan mu da ya dawo gida bayan shafe shekaru takwas yana mulki, Buhari mutumin kirki ne ba barawo ba, ya mulke mu yadda ya dace muna cikin farin ciki, lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su yafe masa kura-kuransa.
“Shugaba Tinubu mutum ne mai son mutane, ina da tabbacin zai ci gaba daga inda Buhari ya tsaya.”

Yadda Daura ke Shirin Tarbar Shugaba Buhari Bayan Ya Sauka Daga Mulki

A wani labarin, an ji cewa yayin da Shugaba Buhari ke dab da sauka daga mulki, mutanen Daura sun shirya tarbarsa.

Mai Martaba Sarkin Daura shi ne kan gaba wurin shirye-shiryen bikin wanda zai gudana bayan dawowar Buhari Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel