Arziki Nufin Allah: Jerin Kamfanoni 10 Mallakin Aliko Dangote a Duniya da Ko da Wasa Baku Sani Ba

Arziki Nufin Allah: Jerin Kamfanoni 10 Mallakin Aliko Dangote a Duniya da Ko da Wasa Baku Sani Ba

  • Akwai kamfanoni 10 mallakin fitaccen attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, kuma dan Najeriya, Aliko Dangote da ba kowa ya sani ba
  • Wani sabon rahoto ya bayyana sunayen kamfanonin da kuma irin harkar kasuwancin da suke yi
  • A kwanaki kadan masu zuwa, Dangote zai kaddamar da wata katafariyar matatar man fetur da ya gina a jihar Legas

Aliko Dangote, dan Najeriyan da ya fi kowa kudi a Afrika kuma mamallakin Dangote Group fitacce ne wajen gina kasuwanci da fafutukar hada-hada a fannoni da yawa.

Bloomberg ta ruwaito cewa, rukunin kamfanin Dangote na harkalla ne ta sukari, siminti da kuma wani fannin da ake kira Nascon Allied Industries.

Wadannan kamfanonin sun kafu da kafafunsu a matsayin na gaba-gaba wajen samar da siminti, sukari da kayayyakin abinci a Najeriya da ma bangarori da yawa a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Abin Duniya Ya Jawo Rigima Tsakanin Mashahurin ‘Dan Kasuwan Najeriya da Yaransa

Dangote na da karin kamfanoni 10
Dangote, mai kudin nahiyar Afrika | Hoto: Business Day
Asali: UGC

Sai dai, wani rahoto na baya-bayan nan ya bayyana wasu kamfanoni 10 da ‘yan Najeriya basu sani ba kuma mallakin Dangote ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadannan kamfanoni da ba kowa ya san su ba sun kara adadin miliyoyin daloli ga dukiyar Dangote. Ga su kamar haka:

Twister B.V

Twister B.V wani kamfanin sarrafa gas ne da ke kasar Netherland wanda rukunin kamfanin Dangote ya saye a 2016.

Fasahar kamfanin na sarrafa gas zuwa kayayyakin amfani barkatai da suka hada da iskar gas ta LNG, CNG da NGLs.

Dangote Sinotruk

Kamfanin Dangote ya kirkiri fannin harhada motoci da darajarsa ta kai $100m a 2017 a cikin jihar Legas.

Kamfanin yana nan a Ikeja, kuma hadaka ce tsakanin kamfanin China na manyan motoci; SINOTRUK da Dangote.

Dangote ne ke da 60% na hannun jarin kamfanin, wanda daya bangaren na China yake da sauran kason; 40%.

Kara karanta wannan

Lambar Ministan Buhari Ta Fito, Gwamnatin Tinubu Za Ta Bincike Shi Kan Abubuwa 5

Greenview Development Nigeria Limited (GDNL)

GDNL wani sashe na kamfanin Dangote ne da ke kula da ayyukan Terminal E a tashar jirgin ruwan Legas a yankin Apapa.

Dangote Agro Sacks Limited

Dangote Agro Sack Limited wani kamfani dne a ke saka buhunnan zuba kayayyaki ga kamfanonin Dangote da kuma wasu kamfanonin waje.

Kamfanin na da bangarori uku a Najeriya; a Ikeja, Legas da kuma wani Obajana ta jihar Kogi. Buhunna kala-kala kamfanin ke samarwa.

Bluestar Shipping Lines

Bluestar Shipping Lines an kafa shi ne a 1996 domin yin harkallar shige da ficen kayayyaki daga kasashen waje da jigila a cikin gida.

Kamfanin na da burin gogayya da kamfanoni irinsu Break Bulk, Vessel Berthing da Sailing a duniya.

Saipem Dangote E&C

Saipem Dangote E&C kamfani ne na gine-gine da ya kware wajen manyan ayyukan gini a Afrika.

Harkalla ce tsakanin kamfanin Dangote da kuma wani kamfanin kasar Italia, Saipem wanda aka hada a 2015.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama dillalan kwaya 619 a wani sanannen wuri a birnin Kano

Integrated Steel PLC

Dangote ya sayi kamfanin mola-molan karafa na Oshogbo sama da shekaru 10 da suka gabata.

Kamfanin, wanda a yanzu aka sani da Integrated Steel PLC yana samar da karafan rodi da a shekara ke iya samar da tan sama da 400,000.

DIL Power Limited

DIL Power Limited ne ke aikin samar da wutar lantarki ga kamfanin mai na Dangote, inda yake samar da wutar da ta kai 400MW.

Dangote Granite Mines Limited

Wannan kamfanin ke aikin hakar duwatsun kankere masu daraja a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Dangote Coal Mines Limited

Dangote Coal Mines Limited (DCM) wani kamfanin hako ne da ke aikin hakar gawayin kwal daraja da ke nan a jihar Kogi a Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Dangote zai kaddamar da matatar mai

A halin da ake ciki, kafin saukar shugaba Buhari, Dangote zai kaddamar da matatar man fetur da ya gina a jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana yadda kamfanin zai yi tasiri wajen sauya akalar man fetur da yadda ake tace shi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel