NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Ta Kama Dillalan Miyagun Kwayoyi Sama da 600 a Jihar Kano

NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Ta Kama Dillalan Miyagun Kwayoyi Sama da 600 a Jihar Kano

  • Rundunar NDLEA a jihar Kano ta yi nasarar kame masu safarar kwayoyi a jihar da ke Arewa maso Yamma
  • Tuni an gurfanar da su a kotu, inda za su fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata na laifi
  • Ya zuwa yanzu, an ce akalla mutum miliyan 2 ne a jihar Kano ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi

Jihar Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta yi nasarar kame wasu bata garin da ake zargin suna harkallar miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Rahoton da muke samu daga Channels Tv ya bayyana cewa, akalla mutane 619 ne aka kama da miyagun kwayoyin a yankin Sabon Gari da ke jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin din.

Kara karanta wannan

Ahaf: Ana tsaka da yunwa a Najeriya, kwastam sun kama shinkafa da man gyaran kasar waje

Yadda aka kama dillalan kwaya a jihar Kano
An kama masu safarar miyagun kwayoyi a jihar Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Dillalai aka kama masu siyar da miyagun kwayoyi

A cewar, wadanda aka kama din ba kawai masu shan kwaya bane, an kama wadanda ke dillacin miyagun kwayoyin ne tare da kwace wasu kayayyaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato sun fi karfin a ce na mashaya kwayoyin ne, sun fi kama da na wadanda ke dillacin miyagun kwayoyi a jihar.

Ya kara da cewa, wadanda aka kaman tuni aka bincike su kana aka mika su ga kotu domin tabbatar da adalci da hukunci a kansu.

A kalamansa:

“Da yardar Allah mun yi nasarar gurfanar da wadanda ake zargi 619. Idan ina magana a kan wadanda ake zargi, ina nufin wadanda aka kama, aka bincika kana aka gurfanar, ba wai kawai mashaya ba.
“Ba wai irin wadanda ake kama wa da daya biyu na miyagun kwayoyi ba, ina magana ne kan dillalai masu siyar da mai yawa wadanda su ne muka gurfanar da 619.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

Yadda lamarin shan kwaya yake a jihar Kano

Bincike ya bayyana cewa, akalla mutane sama da miliyan 2 ne ke kwankwadar kayan bugarwa a jihar Kano, wanda ke wakiltar sama da kaso 16% na mazauna jihar.

Hukumar NDLEA na ci gaba da kokarinta wajen kamawa da gurfanar da masu shaye-shaye da dillalan miyagun kwayoyi a jihar.

A gefe guda, ana ci gaba da ladabtarwa da daura tubabbun ‘yan shaye-shaye a turbar daina shan kwaya kwata-kwata a gidan gyaran hali a jihar.

Ganduje Ya Yi Wa Abba Gida-Gida Martani Mai Zafi Kan Sukar Tinubu

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki magajinsa, gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa sukar shirin N500bn na tallafin Shugaba Tinubu domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Idan za a tuna dai Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kano ta yi korafi kan rabon tallafin N500bn domin masu kananan sana'o'i.

Kara karanta wannan

Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel