“Zan Duba Yiwuwar Daukar Mataki Na Gaba”: FBI Ta Ki Amincewa Da Bukatar Dan a Mutun Obi Na Game da Tinubu

“Zan Duba Yiwuwar Daukar Mataki Na Gaba”: FBI Ta Ki Amincewa Da Bukatar Dan a Mutun Obi Na Game da Tinubu

  • Jeffrey Guterman, wani dan kasar Amurka mai goyon bayan Peter Obi ya ce hukumar FBI ta ki amincewa da bukatarsa game da duba fayal mai dauke da bayanan Tinubu
  • Guterman ya nemi sanin karin bayani game da kudade $460,000 biyo bayan kitimurmurar harkallar kwaya ta 1993 game da Tinubu
  • Mutumin ya ce zai sake duba wata hanyar tuntubar FBI don tabbatar da samun bayanai da masaniya game da zababben shugaban Najeriya

Kasar Amurka Wani dan kasar Amurka, Jeffrey Guterman kuma masoyin Peter Obi na Labout ya ce, hukumar binciken laifuka ta FBI a Amurka ta ki ba shi damar duba bayanai game da Bola Ahmad Tinubu.

Guterman, wanda tsohon ma’aikacin lafiya ne ya nemi a bashi bayanai da dauke da yadda aka kaya da batun kudade $460,000 biyon bayan kitimurmurar harkallar kwaya ta Tinubu a Amurka a 1993.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

Hukumar ta FBI ta ki amincewa da bude sirrin fayal din Tinubu, inda ta kafa hujja da cewa, hakan zai zama ba da bayanai na sirrin wani ga wani da bai dace ba.

Wani zai tona asirin Tinubu a Amurka
Yadda bature ke son tonon asirin Tinubu | Hoto: @JeffreyGuterman
Asali: UGC

Ya saba ka’ida mu saki bayanai sakaka

Hakazalika, hukumar ta bayyana cewa, bukatar dan a mutun Obi ta saba da ka’idar aikinsu da kuma tsarinsu na kiyaye bayanan sirri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rubutun da ya yada a Twitter, Guterman ya yada takardar da FBI ta bashi a matsayin martani ga bukatarsa ta ganin bayanan Tinubu.

A bangare guda, Guterman ya ce FBI ta ambaci cikakken sunan Tinubu kamar haka: “TINUBU, BOLA AHMED” a cikin wasikarsu, har da sunansa na tsakiya, wanda bai ambata ba a wasikar da ya tura musu.

FBI na da bayanai game da $460,000 na harkallar Tinubu

Ya kuma bayyana cewa, batu ne sananne cewa FBI na rike da fayal din da ke ishara ga batun kudaden da yake magana akansu game da Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tasa Keyar Jami'in Bogi Na EFCC Zuwa Gidan Gyaran Hali

Duk da cewa bai bayyana abin da zai yi ba a nan gaba, ya ce ba zai sake tura wata bukata ta wasika ga FBI ba, amma zai san na yi don zai nemi wata hanyar.

Bola Ahmad Tinubu dai ya zama shugaban kasa a Najeriya, kuma nan da kwanaki kadan za a rantsar dashi don maye gurbin Buhari.

Tuni ake yada jita-jita game da wadanda zai yi aiki dasu, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, duk da gwamnan ya sha karyata hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel