NDLEA Ta Faɗa Wa Kotu Gaskiya Kan Karar da PDP Ta Shigar da Tinubu

NDLEA Ta Faɗa Wa Kotu Gaskiya Kan Karar da PDP Ta Shigar da Tinubu

  • Hukumar NDLEA ta soki karar da jam'iyyar PDP da babban jigonta, Sanata Dimo Melaye suka shigar da Tinubu a Kotu
  • Hukumar ta ce ko da wasa ba ta taba ganin sunan Tinubu a sunayen da Amurka ke turo mata masu hannu a baɗakalar miyagun kwayoyi
  • PDP da Melaye sun garzaya babbar kotun tarayya a Abuja suna neman ta tilasta wa NDLEA ta damke Tinubu

Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta roki babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar kan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

PDP da Sanata Dino Melaye sun shigar da ƙara gaban Kotun suna neman a tilastawa NDLEA ta kama kana ta gurfanar da Tinubu kan zargin badaƙalar kuɗi masu alaƙa da safarar miyagun kwayoyi a Amurka.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Ɗaliban Jami'a a Najeriya, Rayuka Sun Salwanta

Asiwaju Bola Tinubu.
NDLE Ya Faɗa Wa Kotun Gaskiya Kan Karar da PDP Ta Shigar da Tinubu Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

The Cable ta rahoto cewa jawabin share fagen fara shari'a, NDLEA ta roki babbar Kotun da ƙori karar saboda ko kaɗan ba ta dace ba.

Joseph Sunday, daraktan sashin shari'a na hukumar NDLEA, ya shaida wa Kotun ranar Laraba cewa ƙarar da PDP da Melaye suka shigar bata lokaci ne kuma Kotu ba ta da hurumin sauraronta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NDLEA ta ƙara da cewa ya kamata kotu ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar adawa kan batun saboda, "Adawar siyasa ce," amma ba bu yawun yan Najeriya.

Hukumar yaƙi da fatauncin miyagun kwayoyin ta ƙara da cewa ƙarar wani makircin ne da nufin soke sahihancin takarar Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Muna da alaƙa mai kyau da Amurka - NDLEA

A wata takardan Afidabit da ke goyon bayan jawabin farko, Chia Depunn, jami'in sashin shari'a na NDLEA, ya ce hukumar na da alaƙa mai tsafta tsakaninta da gwamnatin Amurka.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Yanke Shiyyar da Zata Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10? Gaskiya Ta Yi Halinta

Haka zalika ya bayyana cewa ba su taba ganin sunan Tinubu cikin sunayen da suke tura wa juna kan badaƙalar kwayoyi tsakanin Najeriya da ƙasar Amurka.

A ruwayar Punch, Ya ce:

"NDLEA na da alaƙa mai kwari da gwamnatin ƙasar Amurka, sunan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta kowace diffa ko haɗin sunaye da shiga rububi, bai taɓa fitowa a musayar sunayen masu laifi tsakanin mu da Amurka ba."

"Ku Hada Hannu da Tinubu," Lawan Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi

A wani labarin kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya shawarci Atiku da Peter Obi su maida wuƙarsu kube

Sanata Ahmad Lawan ya jawo hankalin Atiku Abubakar da Peter Obi, Ya ce babu sauran faɗa tunda zabe ya wuce, su taho a haɗa hannu don ci gaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel