Mutum 7 da Buhari Ya Ba Mukami, Kafin a Je Ko Ina Ya Canza Shawara, Ya Sallame Su

Mutum 7 da Buhari Ya Ba Mukami, Kafin a Je Ko Ina Ya Canza Shawara, Ya Sallame Su

Abuja - Bisa al’ada idan aka nada mutum ga kujerar gwamnati, ana sa ran ya kammala wa’adinsa kafin ya sauka, ko akalla dalili ya jawo korarsa.

Akwai wasu da Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari ya kora ko kuma ya janye mukamin da ya ba su alhali ba su dade da hawa kan kujerar iko ba.

Haka zalika akwai wasu da aka sallama daga ofis su na matsayin rikon kwarya.

Rahoton nan na Legit.ng Hausa ya tattaro fitattun irin wadannan abubuwa da suka faru tun daga lokacin da aka rantsar da Gwamnati mai ci zuwa yau.

1. Ahmed Musa Ibeto

A 2015, Gwamnatin tarayya ta janye nadin da ta nemi ayi wa Ahmed Musa Ibeto a matsayin Minista, aka maye gurbinsa da Abubakar Bawa Bwari.

Watakila an yi hakan ne bayan ganin Gwamnan Neja da Ahmed Ibeto sun fito daga yanki guda, daga baya aka ba shi kujerar Jakada zuwa Afrika ta Kudu.

Kara karanta wannan

Waiwaye Ga Mulkin Buhari: Manyan Alkawura 3 Da Buhari Ya Dauka, Amma Ya Gaza Cika Wa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Ibrahim Magu

A lokacin da yake kan kujerar EFCC a matsayin shugaban rikon kwarya, Muhammadu Buhari ya dakatar da Ibrahim Magu daga aiki, aka yi waje da shi.

Har Magu ya bar ofis, bai rike shugabancin hukumar EFCC a matsayin mukaddashin shugaba ba.

3. Lauretta Onochie

Majalisar dattawa ta ki yarda ta tantance Lauretta Onochie a matsayin Kwamishinar hukumar zabe ta INEC, jama’a su na zargin ta na da ra’ayin siyasa.

Majalisa ta ce amincewa da nadin Onochie zai zama rashin adalci. A karshe dole shugaban kasa ya janye mukamin da ya nemi a ba ta, ya kai ta NDDC.

Buhari
Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

4. Mojisola Yaya-Kolade

A farkon 2022, wasika ta fito daga fadar shugaban kasa cewa ana so a canza Dr. Mojisola Yaya-Kolade a majalisar da ke sa ido a kan aikin hukumar ICPC.

Hakan yana zuwa ne ‘yan kwanaki da Muhammadu Buhari ya bada sunanta. A karshe haka aka maye gurbinta kafin ta shiga ofis da AIG Olugbenga Adeyanju.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Bar APC Da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

5. Hadiza Bala Usman

A farkon 2021, Mai girma Shugaban kasa ya amince Hadiza Bala Usman ta kara shekaru biyar a matsayin shugaban NPA mai kula da tashoshin ruwa na kasa.

Bayan watanni kusan hudu, sai Muhammadu Buhari ya dakatar da Bala Usman a dalilin sabaninta da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, haka ta bar ofis kwatsam.

6. Mohammed Sani

Kwanakin baya Sakataren gwamnatin tarayya ya fitar da sanarwa cewa an karawa Mohammed Sani wa’adi, zai kara shekaru biyu yana rike da hukumar NASENI.

Bayan ‘dan lokaci sai ga sabuwar sanarwa cewa Shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar, aka umarci Farfesa Mohammed Sani Haruna ya zama shugaban riko.

7. Ifeanyi Ararume

A Satumban 2021, kowa ya ji labarin an nada tsohon Sanatan Imo ta Arewa, Ifeanyi Ararume ya shiga cikin majalisar da ke sa ido a aikin kamfanin mai na NNPCL.

Kafin Ararume ya fara cin moriyar ofis sai aka bada sanarwar fatattakarsa, aka canza shi da Margaret Chuba Okadigbo, ana da labarin hakan ya jawo ya tafi kotu.

Kara karanta wannan

An Yi Asarar Rayukan Bayin Allah Yayin da Rigima Ta Kaure Tsakanin Mazauna Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel