An Yi Asarar Rayukan Bayin Allah Yayin da Rigima Ta Kaure Tsakanin Mazauna Abuja

An Yi Asarar Rayukan Bayin Allah Yayin da Rigima Ta Kaure Tsakanin Mazauna Abuja

  • Direbobin Keke Napep da ke aiki a garin Abuja sun samu sabani, hakan ya jawo mummunan artabu
  • A halin yanzu ana cigaba da fada tsakanin wasu Hausawa da Gwarawan da suke rayuwa a Gwarimpa
  • Majiyoyi sun nuna a ranar Asabar rigimar ta fara, har zuwa yanzu ba a iya shawo kan lamarin ba

Abuja - Rigima ta barke tsakanin wasu Hausawa da Gwarawa da ke tuka Keke Napep, abin ya faru ne da safiyar Litinin a garin Abuja.

Rahoton da muka samu daga Punch ya ce rikicin ya barke ne a yankin 3rd Avenue da ke Unguwar Gwarinpa a babban birnin tarayya.

Bidiyoyi na yawo a kafofin sada zumunta da ke nuna wasu sun samu rauni. Legit.ng Hausa ba za ta iya tabbatar da ingancin bidiyoyin ba.

Jaridar ta ce wani daga cikin mazauna Gwarinpa ya shaida mata sabanin tsakanin Hausawa ne da Gwarawa da ake ganin su ne ‘yan gari.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Mutane su na cikin dar-dar

Majiyar ta ce lamarin ya kai mutane sun gagara fita waje saboda gudun an yi masu lahani, baya ga haka akwai wadanda suka samu rauni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi kokarin tuntubar Kakakin ‘yan sandan reshen Abuja, SP Josephine Adeh, amma ba a dace ba, jami’an tsaron ba su amsa waya ba.

Abuja
Jami'an tsaro a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A rahoton da Vanguard ta fitar, ta ce rikicin ya fara ne tun a karshen makon da ya gabata, aka shigo har makon nan abin ya gagara lafawa.

Ana kishin-kishin cewa silar rigimar ita ce wasu matasan Hausawa da ke saida miyagun kwayoyi sun yi yunkurin yin fasahi a wani gida.

Gidan da aka nemi a kutsa na wani Kansila ne a mazabar Gwarimpa, hakan ya jawo rikici tsakanin bakin da kuma mazaunan wannan yanki.

Wasu wanda suka shaida abin da idanunsu, sun zanta da Vanguard, suka shaida cewa an kashe mutane akalla uku a sanadiyyar rigimar.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallaci A Ranar Sallar Idi

Baya ga mutanen da aka hallaka, an yi wa wasu rauni, sannan an yi asarar motocin hawa.

Jami’an tsaro sun yi kokarin kwantar da hankali tare da kawo zaman lafiya a ranar Asabar, zuwa yau kuma sai abin ya sake jagwalgwalewa.

Tinubu zai iso Abuja

Rahoto ya zo cewa Hon. James Faleke ya fadi lokacin da jirgin shugaban mai jiran gado zai sauka a birnin Abuja baya shafe wata a garin Abuja.

An gayyaci mutanen da ke Birnin Tarayya da Nasarawa su fito tarbar Bola Tinubu da karfe 2:00 a babban filin jirgin sama na Nnamadi Arzikwe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel