Jerin Irin Tufafin Da Aka Haramta Saka Wa A Jami'ar Calabar

Jerin Irin Tufafin Da Aka Haramta Saka Wa A Jami'ar Calabar

  • Jami'ar Calabar ta haramta sanya wasu nau'in suturu a makarantar
  • Hukumar sadarwar makarantar UNICAL, SERVICOM ce ta sanar da haka biyo bayan karuwar shigar rashin da'a tsakanin dalibai da wasu malamai mata
  • Jami'ar ta ce dokar hana sanya nau'in kayan zai fara daga Talata, 2 ga watan Mayu

Calabar, Jihar Cross River - Hukumar jami'ar Calabar (UNICAL) ta kirkiro dokar sanya tufafi a kokarin rage rashin da'a tsakanin malamai da dalibai.

Farfesa Patrick Egaga, daraktan SERVICOM na jami'ar, ya bayyana damuwarsa kan shigar rashin da'ar, musamman tsakanin dalibai da wasu malamai mata, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Jami'a
Jerin Irin Tufafin Da Aka Haramta Saka Wa A Jami'ar Calabar. Hoto: Naija_PR
Asali: Twitter

Jerin shiga da aka haramta a Jami'ar Calabar (UNICAL)

1. Gajeren siket ko tufafi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zargin Ta'addanci: Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokoki a Arewa Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabo

2. Riga da bai rufe gwiwa ba, tufafi mai budaden baya da irinsu

3. Spaghetti finger

4. Riguna masu gajeren hannu

5. Handless gowns

6. Bikinis masu nuna sura ko siffan jiki

7. Bum shorts masu nuna cinya

8. Split-skirts

9. Kaya masu matse jiki

10. Riguna masu wuyar V da ke nuna 'tsiraici'

11. Tubes, strip-less

12. Dagargajajen jeans

13. Shorts above the knee

14. Riguna marasa hannu

15. Singlets Lingeries

16. Zazzage wanduna da wasunsu.

Dokar za ta fara daga 2 ga watan Mayu

Jami'ar ta sanar da Talata, 2 ga watan Mayu a matsayin ranar da dokar za ta fara aiki.

Duk dalibin da ya zo da irin shigar ba zai "shiga harabar makaranta ba ko kuma ya karbi hukuncin da ya dace."

"Ba za mu juri irin wannan a cikin jami'ar ba daga Talata 2 ga watan Mayu 2023," in ji Farfesa Egaga.

Kara karanta wannan

A Watan Azumi, Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigan PDP 2 Sun Shiga Tsaka Mai Wuya

"Za a kafa jami'an tsaro hadin gwiwa da hukumar gudanarwa don tabbatar da bin dokar" in ji shi.

An bukaci dalibai mata na jami'ar UNICAL da su kwaikwayi shigar shugabar jami'ar

Farfesa Egaga ya ce akwai bukatar dalibai da malamai mata da su kwaikwayi shigar shugabar jami'ar, Farfesa Florence Obi, da mataimakanta, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga dalibai maza da malamai da su yi koyi da salon shigar shugaban gudanarwar jami'ar, Janar Martin Luther-Agwai mai ritaya, da kuma rajistara, Mista Gabriel Egbe.

Gwamnan Anambra Ya Rufe Gidajen Caca Da Wasanni

A wani rahoton, gwamnatin jihar Anambra ta bada umurnin rufe dukkan gidajen caca da gidajen wasan gyam a jihar.

The Punch ta rahoto cewa gwamnan ya bada umurnin ne bayan samun ayyukan masu aikin damfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel