Obi Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo A Anambra, Ya Bayyana Abin Da Suka Tattauna

Obi Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo A Anambra, Ya Bayyana Abin Da Suka Tattauna

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun gana a ranar Asabar, 25 ga watan Maris a Anambra
  • Obi wanda ya wallafa hotunan haduwarsa a shafinsa na Twitter ya ce sun tattauna kan halin da kasa ke ciki
  • Obasanjo na daya cikin fitattun yan Najeriya wadanda suka fito fili suka nuna goyon bayansu ga takarar Obi a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu inda zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya yi nasara

Awka, Anambra - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, LP, a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Awka, jihar Anambra, a ranar Asabar, 25 ga watan Maris.

Obi wanda tsohon gwamna ne a jihar Anambra ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Lahadi, 26 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Atiku Ya Yi Magana Kan Janye Kararsa Na Kallubalantar Nasarar Bola Tinubu

Peter Obi
Obi Ya Gana Da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo A Anambra. Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta tattaro cewa mutenan biyu sun tafi jihar ta Anambra ne domin halartar bikin ciki shekara guda kan mulki na gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo.

Abin da na tattauna tare da Obasanjo - Peter Obi

Obi ya yi godiya bisa 'hira ba hayaniya' da ya yi da tsohon shugaban kasa Obasanjo a filin tashin jirage na Anambra.

Ya ce sun tattauna kan 'batutuwa da ke faruwa a kasar a halin yanzu.'

Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar LP ya rubuta a shafinsa na Twitter:

"Na yi farin ciki bisa lokacin da na samu na tattauna da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a filin tashin jirage na Anambra. Mun tattauna kan batutuwan da ke faruwa a kasa."

Legit.ng ta lura cewa Obasanjo ya goyi bayan takarar shugabancin kasa na Obi a 2023. Obasanjo ya ce duk da cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ba waliyyi bane, ya fi dama-dama idan aka kwatanta shi da sauran yan takarar.

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Amma, Obi ya zo na uku a zaben, ya sha kaye hannun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jigo a jam'iyyar PDP ya yi bankwana da jam'iyya yan awanni kafin zaben gwamna

A wani rahoton, Dele Omenogor, kusa a jam'iyyar PDP a jihar Delta, ya fita daga jam'iyyar ana daf da zaben gwamna na ranar Asabar.

Omenogor ya yi korafi da cewa gwamnatin Ifeanyi Okowa ta mayar da masarautar Amai saniyar ware da garin Ukwuani, hakan ya sa ya bar jam'iyyar ta PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel