Sanadi: Yadda akayi Yaro Dan Shekara 7 Mai Suna Albert Daga Kasar Ghana Ya Zama Sananne a Duniya

Sanadi: Yadda akayi Yaro Dan Shekara 7 Mai Suna Albert Daga Kasar Ghana Ya Zama Sananne a Duniya

  • Kawun yaron shine ya ɗauki faifan vidiyon a cikin gida, yayin da yake daman gursheƙen kuka
  • Yaron yana kuka akan an bashi ayaba yaci a maimakon doya da yake so yaci, kakar yaron tayi masa waƙa yana kuka, sai ya kece da dariya.
  • Sh kuma Kawun yaron ya Saida wayar, wanda ya saya ya ɗaura vidiyon ɗaura a kafar sadarwa ta zamani

Idan ɗaukaka tazowa mutum, to ko shakka babu, ko yana ƙasa ta bakwai ne sai an san shi a ko ina.

Domin ita ɗaukaka, Allah ne yake bada ita, ga wanda yaso kuma a lokacin da yaso.

Bugu da ƙari, sanadin ɗaukaka baya kaɗan, wani mutum yana sane, wani lokacin sai dai mutum yaji shi cikin ta tsundum.

Nketia
Sanadi: Yadda akayi Yaro Dan Shekara 7 Mai Suna Albert Daga Kasar Ghana Ya Zama Sananne a Duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

Magana ake akan yaron nan Albert Ofosu Nketia wanda ya watsu a kafar sadarwa ta zamani akan wani vidiyo da yake ta tafka tashe.

Bidiyon ya ɗauki lokaci ana yayin sa birni da da ƙauye.

Babban abin jan hankali a faifan vidiyon shine yadda yaron yayi amfani da wani salo na canja yanayi daga kuka zuwa dariya cikin ƙiftawar ido.

Shine Menene Dalilin Da Yasa Ya Canja Daga Kuka Zuwan Dariya?

A wata tattaunawa da manema labarai suka yi da mahaifiyar yaron mai suna Rosina, ta bayyana dalilin da yasa yaron yake kuka da har takai ga ɗaukar faifan vidiyon sa.

Mahaifiyar yaron tace, Albert ya addabe su da kuka ne a wannan ranar saboda an hana shi an bashi ayaba yaci a maimakon doya da yake biɗa.

Yana zabga kukan nan ne, sai kakar shi ta soma rera masa wata waƙa irin tasu ta tsofaffi domin ta lallashe shi.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Bidiyon Wata Mata Dauke Da Tagwaye Tana Tallar Ruwan Leda Ya Sanya Mutane Kwalla, Tace Mahaifin Su Ya Gudu

Nketia
Sanadi: Yadda akayi Yaro Dan Shekara 7 Mai Suna Albert Daga Kasar Ghana Ya Zama Sananne a Duniya Hoto: Senior Pikin
Asali: UGC

Nan da nan waƙar ta bashi dariya, a yayin daya fashe da dariya yana cikin zabga kuka ba tare daya sani ba.

Kawu a wajen yaron, shine wanda ya naɗi faifan vidiyon a wayar sa lokacin da abin yake faruwa.

Kuma ya naɗi vidiyon ne bada manufar ya ɗaura shi akan yanar gizo gizo ba ya naɗa ne kawai ya ajiye a wayar sa.

To abin ka da ƙaddara, sai kawun yaron ya siyar da wayar tasa.

Shi kuma wanda ya sayi wayar, sai yaga vidiyon ya burge shi, kawai sai ya ɗaura shi akan yanar gizo gizo.

Koda ɗaura vidiyon, sai ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, inda ba batun da ake sai na vidiyon tare da sarrafa shi zuwa salon barkwanci iri iri.

Yanzu haka faifan vidiyon an kalle shi sama da miliyan 100 a dandalin sadarwa na TikTok kawai banda saura kafafe.

Yayin da yaro Albert ke kuka da canja salo zuwa dariya nan take, hakan yasa ya zama sananne a ƙasar sa ta Ghana, Africa da duniya gabaki ɗaya.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70

Yarinya ta shiga saka kanta a wani guri tsukakke ta rasa yadda zatayi

A wani labari mai kama da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda wata yarinya ƙarama ta saka kanta cikin wani waje tsukakke ta kasa cirewa.

Koda ta kasa cirewa, sai yarinya ta kira mahaifiyar ta domin ta cire mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel