Jiragen Helikwafta 2 Na Rundunar Soji Sun Yi Hadari, Ana Fargabar Rasa Rayuka

Jiragen Helikwafta 2 Na Rundunar Soji Sun Yi Hadari, Ana Fargabar Rasa Rayuka

  • Jirage biyu mallakin rundunar sojin ƙasar Amurka sun yi hatsari kuma ana fargabar mutane da yawa sun mutu
  • Hukumomi a kasar sun ce tuni jami'ai suka kai ɗauki wurin da lamarin ya faru, haɗarin ya auku a daren jiya Laraba
  • Gwamnan Kentucky, Andy Beshear, ya ce sun samu labarin abinda ya faru amma babu daɗin ji

Jiragen Helikwafta guda biyu na rundunar sojin ƙasar Amurka sun yi hatsari yayin da suke shawagin ɗaukar horo a Kentucky ranar Laraba da daddare.

Daily Trust ta tattaro cewa ana fargabar mutane da yawa sun mutu a hatsarin, wanda jami'an US suka ce ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na dare a agogon Amurka.

Jirage masu saukar Angulu.
Jiragen Heƙikwafta 2 Na Rundunar Soji Sun Yi Hadari, Ana Fargabar Rasa Rayuka Hoto: thecable
Asali: UGC

Hukumar 'yan sandan birnin Kentucky ta tabbatar da cewa jami'anta, sojojin bincike da sauran hukumomin tsaro sun mamaye wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya 4 Sun Mutu a Hanyarsu Ta Zuwa Abuja, Wasu 13 Sun Jikkata

Rundunar sojin saman Amurka 101st Airborne Division, ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna tabbatar da cewa jirage biyu daga sashin runduna ta 101 sun yi haɗari a daren jiya wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama."
"A halin yanzun mun maida hankali kan Sojojin da haɗarin ya rutsa da su da kuma iyalansu."

Haka nan da yake tsokaci, gwamnan Kentucky, Andy Beshear, ya yi kira ga mutane su sanya waɗanda haɗarin ya shafa cikin Addu'a domin ana tsammanin abun ya yi muni.

Ya ce jami'an 'yan sanda da kuma jami'an yankin sun kai ɗauki wurin da jiragen suka faɗo.

"Mun samu labari mara daɗi daga Fort Campbell, rahoton farko ya ƙunshi cewa jirgin Helikwafta ne ya yi hatsari tare da ana tsammanin rasa rayuka da dama," gwamnan ya wallafa a shafinsa.

Kara karanta wannan

Sabbin Bayanai: Babban Tasirin da Canjin Kuɗi Ya Yi Kan 'Yan Bindiga, Masu Garkuwa da Yan Siyasa

Gwamnan ya ƙara da cewa suna dakon samun cikakkun bayanai nan gaba bayan kammala bincike kan abinda ya faru.

Wani Basarake a Jihar Gombe Ya Rasa Biyu Daga Cin Yan Uwansa a Hatsari

A wani gefen kuma, Haɗarin Mota ya yi ajalin yan uwan babban Basarake a jihar Gombe yayin da suke hanyar zuwa Kaduna.

Bayanai sun nuna cewa matar Galadiman Tangale da ɗan yayansa sun rasu a hatsarin mota da ya rusta da su.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya tura tawagar wakilai da ta ƙunshi manyan kusoshin gwamnati domin yi wa hakimin ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel