An Kashe Wasu Mutum 5 da Ke Kamun Kifi a Wani Yankin Jihar Benue

An Kashe Wasu Mutum 5 da Ke Kamun Kifi a Wani Yankin Jihar Benue

  • Rahoton da muke samu daga jihar Benue ya bayyana cewa, wasu ‘yan kutse sun hallaka mutane biyar a wasu yankunan jihar
  • Ana zargin Fulani makiyaya da kai wannan harin da ya yi sanadiyyar mace-mace, inda aka ce har da mata uku daga cikin wadanda suka mutu
  • ‘Yan sanda sun ce basu samu labari ba, amma majiyar yankin ta bayyana yadda lamarin ya faru dalla-dalla a makon jiya

Jihar Benue - Mutum biyar aka kashe a karshen makon da ya gabata a lokacin da wasu ‘yan kutse suka farmaki karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

A cewar mazauna yankin, an kashe hudu daga cikin mutanen ne a kududdufin kamun kifi da ke gundumar Nyiev yayin da dayan kuma aka kashe shi a garin Chongu da ke karamar hukumar ta Guma.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun harbe jami'an gwamnati na NSCDC 3, a wata jiha

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, an kashe wani mai suna Tyowoofa Iorpuu mai shekaru 45 da ‘ya’ya biyar a ranar Lahadi da rana a garin Chongu.

Yadda aka kashe wasu mutane a jihar Benue
Jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Meye hukumomi suka ce game da harin?

Shugaban tawagar tsaro a Guma, Christopher Waku ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, mutum hudun kuma, ciki har da mata uku da namiji daya an kashe su ne a ranar Alhamis a lokacin da suke kamun kifi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waku ya kara da cewa, ‘yan kutsen sun hallaka wani mutum a yankin Chongu da ke gundumar Mbawa, inda yace mashekan ana zargin Fulani ne makiyaya, rahoton Punch.

An tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, inda tace har yanzu dai bata samu labarin abin da ya faru ba.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Ana yawan samun hare-hare a jihar Benue, inda gwamnatin jihar ke yawan zargin Fulani makiyaya da farmakar al’ummar jiharsa haka siddan babu dalili.

An kashe jami’an tsaro 3 da fararen hula 2

A wani labarin, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan ta’adda suka hallaka jami’an tsaro na hukumar NSCDC a wani yankin jihar Imo.

Rahoto ya bayyana cewa, sun kuma hallaka wasu fararen hula biyu da ke gefe basu ji ba basu gani ba a lokacin da suka kai farmakin.

Ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda hukumar NSCDC kuwa har yanzu bata ce komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel