Gwamnatin Amurka ta Karbe Naira Biliyan 25 Daga Hannun Tsohuwar Ministar Najeriya

Gwamnatin Amurka ta Karbe Naira Biliyan 25 Daga Hannun Tsohuwar Ministar Najeriya

  • Tsohuwar ministar albarkatun man fetur a Najeriya ta sake samun kan ta a matsalar badakalar kudi
  • An samu Diezani Alison-Madueke da hannu wajen karbar cin hancin Kolawole Aluko da Olajide Omokore
  • Kolawole Aluko da Olajide Omokore sun yi hakan ne domin samun kwangiloli daga gwamnatin tarayya

America - A ranar Litinin, BBC ta ce Ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka ta bada sanarwar cin ma matsaya a kan shari’o’i biyu domin karbe kadarorin sata.

Sanarwar ta ce ana zargin an mallaki kadarorin nan ne ta hanyar almundaha da aka tafka a Amurka wanda Misis Diezani Alison-Madueke ta na da hannu a ciki.

Baya ga tsohuwar Ministar man ta Najeriya, ana tuhumar ‘yan kasuwan nan Olajide Omokore da kuma Kolawole Akanni da hannu a badakalar rashin gaskiyar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

A karshen shari’ar da aka yi, ma’aikatar kasar Amurkar tayi nasarar karbe kusan tsabar kudi har fam Dala miliyan $53.1 daga wadanda ake tuhuma da laifi.

Takardun kotu sun yi fallasa

Kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a makon nan, jawabin da ya fito daga ma’aikatar ya nuna za a iya sake samun wasu Dala miliyan 16.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takardun kotu da aka samu sun nuna Kolawole Akanni Aluko da Olajide Omokore sun hada-kai, sun biya Madam Alison-Madueke cin hancin dalolin kudi.

Diezani Alison-Madueke
Tsohuwar Ministar mai, Diezani Alison-Madueke Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ita kuma Alison-Madueke wanda ta rike Ministar harkokin man fetur tayi amfani da ofishinta wajen bada kwangilolin Dala miliyan 100 ga Aluko da Omokore.

Da kudin ne rahoton na BBC Hausa ya ce an yi amfani wajen sayan manyan kadarori a Amurka.

Daga cikin kadarorin da aka mallaka har da rukunin wasu gidaje a biranen Kalifoniya da New York da Galactica Star da wani katafaren jirgin ruwa.

Kara karanta wannan

2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

An kuma yi amfani da wadannan dukiyoyi wajen karbawa Aluko da kamfanin Shell bashin banki

The Cable ta ce wannan nasara da aka samu yana cikin kokarin da gwamnatin Amurka ta ke yi na maganin masu tara dukiya ta hanyar almundahana.

Karin albashi a Najeriya

Idan muka dawo gida, rahoto ya zo a baya cewa an kawo dokar da ta ce dole ne gwamnati mai zuwa ta canza mafi karancin albashi daga N30, 000.

Ministan kwadago, Chris Ngige ya nuna daga watan Mayun da Bola Tinubu zai hau mulki za a fara shirye-shiryen karawa ma’aikatan gwamnati albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel