Wajibi ne Idan Tinubu Ya Hau Mulki, Ya Karawa Ma’aikata Albashi – Ministan Buhari

Wajibi ne Idan Tinubu Ya Hau Mulki, Ya Karawa Ma’aikata Albashi – Ministan Buhari

  • Sanata Chris Ngige zai ba Gwamnati mai-zuwa shawarar ta fara shirin yin nazari kan albashin ma’aikata
  • Ministan kwadago da ayyukan Najeriya ya ce yanzu duk bayan shekaru biyar, sai an yi karin albashi
  • 2019 ne lokacin da aka yi karin karshe, saboda haka dole ne za a sake nazarin albashin kafin 2024

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyuka a Najeriya, Chris Ngige ya ce ya kamata zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya duba batun albashi.

Tashar talabijin Channels ta rahoto Dr. Chris Ngige yana cewa kyau da zarar Bola Tinubu ya shiga ofis, gwamnatinsa ta fara shirin kara albashin ma’aikata.

Da aka yi hira da shi a ranar Laraba, Ministan tarayyan ya ce akwai bukatar gwamnati mai zuwa ta kara mafi karancin albashin kasar daga N30, 000.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An kafa tarihi, kasar Turai ta nada Firayinminista Musulmi a karon farko

A tattaunawarsa da gidan talabijin, Ngige ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince ayi wa manyan ma’aikata karin albashi daga Junairun 2023.

Za a karawa ma'aikata albashi

Rahoton ya ce Ministan ya tabbatar da an yi tanadin karin a cikin kasafin kudin bana, ya ce hakan zai rage radadin tsadar rayuwa da tashin farashi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ngige yana ganin zai yi kyau duk bayan shekaru biyar, gwamnatin Najeriya ta duba albashin ma’aikata, ayi la’akari da halin rayuwa a daidai lokacin.

Gwamnatin Buhari
Ministoci a taron FEC Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Abin da sabuwar doka ta ce

A dalilin haka aka fito da dokar da ta wajabta canza mafi karancin albashi bayan shekaru biyar.

Idan za a tuna, a 2019 gwamnati mai-ci ta kara karancin albashin da ma’aikaci zai karba a wata daga N18, 000 zuwa N30, 000, a 2024 wa’adin zai cika.

Shekara daya kafin Mayun 2024 ya kamata a fara zama a kan maganar yin karin, saboda haka daga Mayun bana ya dace Bola Tinubu ya yi harama.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Daga cikin bayanan da zai ba gwamnati mai zuwa, Ministan kwadagon ya ce akwai batun kafa kwamiti daga Mayun 2023 da zai yi nazari kan albashi.

Punch ta rahoto tsohon Gwamnan na Anambra yana cewa sun yi gyara a kan kudin da ake biyan duk ma’aikatan da su ke kan tsarin CONPSS a Najeriya.

Canjin farashin man fetur

Idan aka yi la’akari da darajar Naira a kasuwar canji, za a koma saida fetur a kan N400, a makon nan aka ji labari kungiyar PENGASSAN ta fadi haka.

PENGASSAN ta ce farashi zai danganta da yadda CBN ya saidawa NNPC Dalar Amurka. A yau ana saidawa jama’a fetur a gidajen mai a kusan N200.

Asali: Legit.ng

Online view pixel