Yadda Haƙo Danyen Mai Zai Taimaki Mutanen Jihar Nasarawa, Gwamna Sule

Yadda Haƙo Danyen Mai Zai Taimaki Mutanen Jihar Nasarawa, Gwamna Sule

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nuna farin cikinsa da fara hako ɗanyen man Fetur a jiharsa
  • Ya ce yadda ya ga matasan Nasarawa sun zage suna aiki a wurin ya sanya shi farin ciki domin ko ba komai sun samu aikin yi
  • Idan baku manta ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da aikin haƙo rijiyar mai a jihar arewa ta tsakiya

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana yadda aikin hako ɗanyen mai zai amfani mazauna jihar da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.

Idan baku manta ba, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da rijiyar mai ta farko a tarihin jihar a tsakiyar Benue Trough, ƙaramar hukumar Obi.

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Da yake bayani a cikin shirin Politics Today na gidan Talabijin ɗin Channels ranar Laraba, gwamna Abdullahi Sule ya ce wasu matasan jihar Nasarawa sun samu aikin yi a wurin.

Sule ya kara da cewa babban abinda ya sanya ya ƙara farin cikin da ci gaban shi ne, bayan aikin da matasa ke yi a wurin, zasu ƙara gogewa da sanin yadda ake aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce lamarin zai taimaka wa mazauna Nasarawa kuma zai ƙara rage wa gwamnati aiki a yunkurinta na rage masu zaman kashe wando.

Vanguard ta rahoto gwamna Sule na cewa:

"Lokacin da muka je gane wa idonmu wurin yau, abinda ya sanya ni farin ciki shi ne, matasan mu na Nasarawa ne kan gab a wurin aikin, kamfanin da ke aikin ya ɗauke su aiki."
"Bayan raba gari da zaman kashe wando, matasan zasu ƙara gogewa su kware kan aiki makamancin wannan, kafin yanzu su mutane ne da basu taɓa ganin yadda ake sarrafa ɗanyen mai ba."
"Yau sun wayi gari suna aiki a rijiyar haƙo man kanta, saboda haka suna samun horo, suna samun kwarewa sannan mu kuma muna amfana da ɗan abinda ba'a rasa ba na tattalin arziki."

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Nasarawa

A wani labarin kuma kun ji yadda tun usuli FG karkashin shugaba Buhari ta kaddamar da rijiyar hako ɗanyen mai ta farko a jihar Nasarawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da rijiyan man, ya ce ci gaban zai haɓaka tattalin arzikin Najeiya ba kaɗan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel