EFCC ta Kuma Gurfanar da Yaron Tsohon Shugaban PDP a Kotu a Kan ‘Satar’ N2.2bn

EFCC ta Kuma Gurfanar da Yaron Tsohon Shugaban PDP a Kotu a Kan ‘Satar’ N2.2bn

  • EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ta koma kotu da Mamman Nasir Ali
  • Ana zargin yaron na Kanal Ahmadu Ali da wani Christian Taylor da badakalar tallafin man fetur
  • Karar ta na gaban kotun laifuffuka na musamman da yake Legas, za a cigaba da shari’a a Mayu

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta ce ta gurfanar da Mamman Nasir Ali da wani a gaban kotu.

Rahoton The Cable ya nuna ana tuhumar Mamman Nasir Ali wanda ‘da ne ga Ahmadu Ali da hannu a wata badakalar N2.2bn ta tallafin fetur.

Mai magana da yawun bakin EFCC ya fitar da jawabi, yana cewa sun taba gurfanar da Mamman Nasir Ali da wani takwaransa a laifi, Christian Taylor.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Hukumar ta ce Nasir Ali da Christian Taylor su na fuskantar shari’a a gaban Alkali Adeniyi Onigbanjo na babban kotun jihar Legas mai zama a Ikeja.

Rashin lafiya ta kama Adeniyi Onigbanjo

Jawabin Wilson Uwujaren ya nuna daga baya Mai shari’a Adeniyi Onigbanjo ya janye hannunsa daga karar a dalilin rashin lafiya da yake fama da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Nation ya ce hakan ya bada dama shari’ar ta je gaban Mojisola Dada na kotun laifuffukan musamman.

EFCC.
Ofishin Hukumar EFCC Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

A halin yanzu an sake gurfanar da su din tare da kamfanin Nasaman Oil Services Limited da zargin aikata laifuffuka 49 da suka sabawa dokokin kasa.

Hukumar ta ce laifuffukan da ke wuyan wadanda ake tuhuma sun kunshi kutun-kutun, karya domin samun kudi, zamba, sata da amfani da takarun bogi.

Kamar yadda EFCC ta ke ikirari, ayyukan mutanen sun sabawa sassa dabam-dabam na dokokin kasa, da suka bayyana gaban Alkali, sun ce ba su da laifi.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Ceto Mutum 201 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Borno Da Kaduna

Za a koma kotu 29 ga watan Mayu

Lauyan gwamnati, S.K. Atteh ya nemi kotu ta sa ranar a za a fara sauraron shari’a, su soma gabatar da shaidu da hujjojin da suke da su domin ayi hukunci.

Lauyan wadanda ake kara, Kolade Obafemi bai iya belinsu ba, EFCC za ta cigaba da tsare su a hannunta. Alkali ya ce sai 29 ga watan Mayu za a awo kotu.

Harin Aondona Dajoh

A makon da ya gabata Aondona Dajoh ya lashe zaben jihohi da INEC ta gudanar a kasa, zai wakilci mazabarsa a majalisar dokoki na jihar Benuwai.

Rahoto ya zo cewa cikin dare wasu miyagu suka rutsa Hon. Dajoh a hanyar komawa gidansa, Honarabul ya ari ta kare, amma dai an kona masa mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel