Abba Gida-Gida: Dalilai 6 Da Suka Sa Dan Takarar NNPP Ya Kayar Da APC A Kano

Abba Gida-Gida: Dalilai 6 Da Suka Sa Dan Takarar NNPP Ya Kayar Da APC A Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, da aka fi sani da Abba Gida-Gida, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

A sakamakon karshe da baturen zabe, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana, Abba Gida-Gida ya samu kuri’u 1,019,602, yayin da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nasir Yusuf Gawuna, ya samu kuri’u 890,705 ya zo na biyu.

Abba Gida-Gida
Zaben Gwamnan Kano: Dalilai Shida Na Nasarar Abba Gida-Gida. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Jimillar kuri’u 2,084,000 aka kada, Abba ya baiwa Gawuna tazara da kuri’u 128,897.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mai sharhi kuma babban malami a kwalejin ilimi ta Kano, Dakta Kabiru Sa’id Sufi ya bayyana zaben a matsayin “ gasa mai kyau ”.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

Ga wasu dalilai da ake ganin sun taimakawa Abba wajen yin nasara

1. Tasirin Kwankwaso a zaben shugaban kasa

Kokarin da Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu na daya daga cikin abubuwan da suka janyo nasarar Abba Kabir Yusuf a zaben da aka kammala, a ra'ayin Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Jagoran kwankwasiyyar ya lashe Jihar Kano a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 da kusan kuri'a miliyan daya inda ya bada tazara sosai ga Tinubu, wanda ya yi na biyu.

Fagge ya ce:

''Kwankwaso madubi ne a siyasa kuma ya na tare da matasa. In ka lissafa, matasa ne yawanci ma su kada kuri'a. Shi yasa matasa suka fito da yawansu don ganin an kai ga nasara.''

2. Rashin gamsuwa da gwamnatin APC

Farfesa Fagge ya kara da cewa rashin gamsuwa da shugabancin APC a jihar da kasa gaba daya ya taimaka wajen tabbatar da nasarar dan takarar NNPP.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo

Ya ce matasa ba su ji dadin dadin wasu dokoki da gwamnatin APC ta bijiro da su ba.

3. Rashin fita zabe

Duk da Kano na da yawan ma su kada kuri'a sama da milyan biyar, amma kuri'a 2,084,000 aka kada a zaben.

Fagge ya yi korafin karancin fitowar ma su kada kuri'a. Saboda haka dole zaben ya kasance haka, duba da cewar yawancin dattijai ba su fita zabe ba.

4. Karin ingancin zabe

Dakta Kabiru Sufi ya ce karin ingancin hanyoyin gudanar da zaben na daya daga cikin abubuwan da suka bai wa Abba Kabir Yusuf.

Ya ce INEC ta kara inganta hanyoyin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha.

Ya ce:

''An fara zabe akan lokaci. Kuma girke jami'an tsaro a kusan kowacce akwatu ya karfafawa mutane gwiwar fitowa ayi zabe."

5. Bukatar chanji

Dakta Sufi ya alakanta nasarar Abba da yadda ma su zabe su ka gaji, inda ya ce mutane na bukatar chanji

Kara karanta wannan

2023: Yadda Ta Kaya da Manyan Masu Neman Takara a Akwatinsu a Zaben Jihohi

Gwamnatin APC a Kano za ta iya yin wa'adin shekara takwas har sau biyu a jere zuwa 29 ga watan Mayu.

An zabi gwamna Abdullahi Umar Ganduje a 2015 ya kuma yi tazarce a 2019.

Dakata Sufi ya bayyana cewa ''akwai lokaci, mutane su na gajiya da wasu shugabanni. Wannan kan sa a fito takara sosai da bukatar chanji. Wannan ma na iya zama dalili."

6. Yakin neman zabe

Dakta Sufi ya bayyana cewa yanayin yakin neman zabe na daya daga cikin dalilan, ya kara da cewa mai cewa jam’iyyar NNPP ta tafi da matasa cikin al'amuranta.

Ya kuma ce da yawa daliban da gwamnatin Kwankwaso ta dauki nauyin yin karatunsu a kasashen waje suna goyon bayan takarar Abba Kabir.

Sufi ya ce:

“Jam’iyyar NNPP ta hanyar hada kai da matasa ta yi ta yin kamfen musamman a kafafen sada zumunta. Hakan ya taimaka matuka.”

An samu rashin jituwa tsakanin wakilan jam'iyyar PDP da APC a Jihar Ogun

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Ganduje Ya Fadawa Kanawa Su Zabi Abba Gida-Gida a Gobe

A wani rahoton, wakilan jam'iyyar All Progressives Congress, APC da na jam'iyyar PDP, sun yi rikici a ranar Lahadi 19 ga watan Maris a cibiyar tattaro sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun na 2023.

Rikicin ya samo asali ne yayin da jam'iyyar APC ta dage cewa wakilai uku za ta tura wurin tattara sakamakon zaben amma wakilin PDP ya ki yarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel