A Dajin Falgore Aka Dauki Bidiyon Ado Doguwa Yana Karba Bindigar AK-47 - DHQ

A Dajin Falgore Aka Dauki Bidiyon Ado Doguwa Yana Karba Bindigar AK-47 - DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta fayyace gaskiyar lamari kan bidiyon Ado Doguwa da ke yawo a soshiyal midiya
  • An dai gano bidiyon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai yana harba bindigar AK-47 karkashin jagorancin soji
  • DHQ ta ce an dauki bidiyon a dajin Falgore ne yayin wani atisayen soji inda aka gayyaci Doguwa a matsayin babban bako

Hedkwatar tsaro (DHQ) ta yi karin haske cewa bidiyon da ke hasko Alhassan Ado Doguwa, yana harba bindigar AK-47 karkashin jagorancin jami'an soji an dauke shi ne a dajin Falgoresansanin sojoji a jihar Kano, rahoton Vanguard.

Ado Doguwa ya kasance shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai daga jihar Kano.

Alhassan Ado Doguwa yana jawabi a majalisa
A Dajin Falgore Aka Dauki Bidiyon Ado Doguwa Yana Karba Bindigar AK-47 - DHQ Hoto: Daily Post
Asali: UGC

An dauki bidiyon Doguwa ne lokacin da aka gayyace shi dajin Falgore

A wata sanarwa da mukaddashin daraktan labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya saki, DHQ ta ce an dauki bidiyon ne a lokacin atisayen Brigad 3 na rundunar soji ind aka gayyaci dan majalisar a matsayin bako na musamman.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Daba Sun Halaka Jigon PDP Kuma Kansila, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sha da Kyar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Channels tv ta nakalto yana cewa:

"An ja hankalin hedkwatar tsaro zuwa ga wani bidiyo da ke yawo a dandalin soshiyal midiya, inda ana gano shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa yana harba bindigar AK 47 karkashin jagorancin jami'an soji.
"Hedkwatar tsaro na burin sanar da cewar wannan wani yunkuri ne da makirai ke yi na bata sunan rundunar sojojin Najeriya a idon mutanen kirki na kasar nan da duniya baki daya. Wannan bidiyo da ake magana a kai a dauke shi ne dajin Falgore na sojoji.
"Yana da matukar muhimmanci mu sanar da cewa idan aka gayyaci manyan kasa ko baki na musamman zuwa irin wannan atisaye, ana karramasu ta hanyar bari su shiga shirin barbi ba tare da nufin horar da su a matsayin maharbako mayar da su kwararru a wajen harbi ba. Bikin harbi wani taro ne da ake yi a duniya kuma ba sabon abu bane a rundunar sojin Najeriya kasancewar manyan kasa da dama sun taba shiga irin wannan shiri a baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Mataimakin Shugaban APC Na Jiha Kwana 2 Gabanin Zabe

"Sai dai kuma, bidiyon Hon Doguwa da ya yadu an wallafa shi ne da nufin bata sunan rundunar sojin Najeriya musamman a wannan lokacin da yan Najeriya da kasashen duniya suka jinjinawa rawar ganin rundunar soji a zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da aka yi.
"Bugu da kari, wasu malamai ma sun saki faifayen murya dauke da fassarar baibai da aka yi wa jawabin da shugaban masu rinjayen a majalisar ya yi a taron. Wannan kagaggen fassara na iya haddasa rikicim, da haifar da fargaba yayin da kasar ke shirin mika gwamnati ga sabuwar zababbiyar gwamnati."

A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindiga sun kwace tare da kona kayan zabe a jihar Bayelsa a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel