'Yan Daban Siyasa Sun Halaka Kansilan PDP a Babban Birnin Jihar Oyo

'Yan Daban Siyasa Sun Halaka Kansilan PDP a Babban Birnin Jihar Oyo

  • 'Yan daban siyasa sun kai hari wurin ralin kamfen jam'iyyar PDP mai mulki a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • Kansilan guduma ta 10 a karamar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas ya rasa ransa a harin na ranar Asabar
  • Kwamishinan yan sanda ya ce sun tura jami'ai yankin domin dawo da zaman lafiya

Ibadan, Oyo State - Wasu tsageru da ake kyautata zaton 'yan daban siyasa ne sun halaka Kansilan jam'iyyar PDP mai wakiltar gunduma ta 10 a ƙaramar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas, Sulaiman Ariyibi.

Jaridar Tribune tace maharan sun yi ajalin jigon jam'iyya mai mulki a jihar Oyo a wurin ralin kamfe wanda ya gudana a Ile Tuntun, gefen Titin Academy, Ibadan ranar Alhamis.

Taswirar jihar Oyo.
'Yan Daban Siyasa Sun Halaka Kansilan PDP a Babban Birnin Jihar Oyo Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Maharan waɗanda ake zaton yan daba ne ɗauke da muggan makamai, sun farmaki jirgin kamfen PDP kana suka yi ajalin Kansilan yayin da sauran suka tsallake rijiya da baya.

An tattaro cewa ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Ibadan ta kudu maso gabas da wasu mambobin PDP da dama sun shallake rijiya da baya, bayan wasu sun basu agaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin PDP na jihar, Injiniya Akeem Olatunji, ya yi zargin cewa ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa ce ta ɗauki nauyin harin.

A kalamansa ya ce:

"Wasu 'yan daban siyasa ne na ɗaya daga cikin manyan jam'iyun adawa suka farmaki wurin da muke kamfe a Ile Tuntun kuma sun halaka Ariyibi, kansilan gunduma ta 10, ƙaramar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas."
"Da yawan magoya bayan mu ciki har da Honorabul Agboworin sun shallake rijiya da baya ta hannun wasu da suka taimaka masu."

Kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo, Adebowale Williams, a wata hira ta wayar salula, ya ce sun tura dakaru yankin domin kama maharan.

A cewarsa, "Har yanzun bamu samu cikakken bayanin abinda ya faru ba amma mun tura dakaru domin su dawo da zaman lafiya a yankin."

LP Da NNPP Sun Cure Wuri Daya da APC Domin Ganin Bayan PDP a Neja

A wani labarin kuma Manyan jam'iyyun adawa guda 2 sun haɗa baƙi, sun ayyana goyon baya ga ɗan takarar gwamnan APC a jihar Neja

Jam'iyyar Labour Party da jam'iyyar NNPP mai kayan alatu sun cure wuri ɗaya, sun ce a yi APC a jihar Neja ranar Asabar mai zuwa.

Sun ce ɗan takarar gwamnan APC, Umar Bago, ne ya cancanta ya ɗora daga inda gwamna mai barin gado zai tsaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel