An Kama Basarake Da Tubabben Mayakin Boko Haram Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

An Kama Basarake Da Tubabben Mayakin Boko Haram Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama miyagun kwayoyi da dama a filin jirgin sama na Murtala Muhammad, da ke Ikeja, Lagos
  • Hukumar ta kuma kama wani tsohon mayakin Boko Haram da tabar wiwi da ta kai kimanin kilo 10 a babban titin Kaduna-Abuja
  • Hukumar ta kuma lalata gonakin tabar wiwi guda uku da girmansu ya haura hekta 30 mallakar wani basarake a garin Kajola da ke iyakar jihohin Ondo da Edo

FCT Abuja - Hukumar NDLEA, ta kama tsohon dan Boko Haram, Alayi Madu; wani mai sarautan gargajya na Kajola, wani gari da ke iyakar jihohin Ondo da Edo, Baale Akinola Adebayo da karin mutum 35 da wasu migayun kwayoyi da nauyinsu ya kai tan 2.2 da hukumar ta kwace filin jirgin saman Murtala Muhammad, da ke Ikeja, Lagos, da kuma sassan jihohi 12 na kasar nan a satikan da suka gabata, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kotu ta Daure Jagororin Jam’iyyar PDP a Kurkuku a Dalilin Cin N140m Saboda Murde Zabe

Kakakin hukumar Femi Babafemi, ya bayyana ranar Lahadi a Abuja cewa Alayi Madu mai shekaru 26, wanda dan Boko Haram ne tsawon shekara 15 kafin daga bisani ya mika kansa ga sojoji a shekarar 2021, ya shiga hannun jami'an NDLEA ranar Alhamis 9 ga watan Maris kan titin Abuja-Kaduna da kilo 10 na tabar wiwi, wanda ya ce ya siyo daga Ibadan, Jihar Oyo, kuma zai kai Maiduguri, Jihar Borno, a cikin buhu.

Jami'an NDLEA
NDLEA ta kama tubabben dan Boko Haram da basarake kan safarar miyagun kwayoyi. Hoto: The Cable

Tubabben dan Boko Haram da aka kama da safarar kwaya

Babafemi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''A bayanin sa, Madu ya ce shi dan garin Banki ne, Jihar Borno kuma ya shiga kungiyar sannannun yan ta'addar, a shekarar 2006 lokacin yana da shekara tara a duniya. Ya ce ya tuba ya kuma mika kansa ga sojoji a shekarar 2021, inda aka kai shi cibiyar wanke zuciya da kawar da munanan akidu a cibiyar Umaru Shehu, Maiduguri da cibiyar Malam sidi, Gombe kafin a sake shi bayan shafe wata shida.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Yaudari Kwararriyar Yar Gidan Magajiya Ya Tura Mata Alat Din N120,000 Na Bogi Bayan Gama 'Harka'

''Daga nan sai ya koma Ibadan, Jihar Oyo inda ya ke tukin babur achaba (Okada) kafin fara safarar har zuwa lokacin da aka kama shi a babban titin Abuja-Kaduna."

Yadda NDLEA ta kama basarake a gonar wiwi cikin dare

A cewarsa, a kokarin hukumar na ganin ta kawo karshen ta'amalli da miyagun kwayoyi a kasa gaba daya kafin zaben gwamnoni, jami'an NDLEA a safiyar Juma'a 10 ga watan Maris, sun yi dirar mikiya a dajin Kajola da ke garin Kajola, wani gari da ke iyakar jihohin Ondo da Edo inda suka lalata gonakin tabar wiwi uku da girman su ya kai hekta 39.801546

Mai gonakin wanda shine Ba'ale na Kajola, Akinola Adebayo, mai shekaru 35, an kama shi cikin gonar da misalin 2:30 na dare, yayin da wasu karin mutum biyu da ake zargin ma'aikatansa ne: Akikuyeri Abdulrahman, mai shekaru 23 da Habibu Olagun, mai shekaru 25, aka kama su a wata bukka kusa da gonar.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Masu Neman Shugabanci a Majalisar Wakilai da Dattawa

A filin jirgin sama na Lagos da ke Ikeja, jami'an sirri sun dakatar da kilo 11.90 na heroine da kuma gram 500 na tabar wiwi da aka boye a cikin firinji, wanda yana cikin kayan da aka aiko daga Afirka ta Kudu ranar Talata 7 ga wata Maris a jirgin Ethiopian airline daga Addis Ababa, Ethiopia.

''Hukumar ta baza karnunka masu gano miyagun kwayoyi don gano in da aka boye kwayoyin a cikin kaya kuma a kankanin lokaci, sun gano katan katan na kwayoyi a cikin firinji,'' a cewar Babafemi.

Ya ce biyar daga cikin wanda ake zargi sun bada gudunmawa wajen safarar kwayoyin kuma an kama direban wata babbar mota da ke da alaka da kwayoyin, da suka hada da Dairo Quam, Oluwaseun Ogunmene, Adeleke Abdulrasaq, Bamidele Adewale da Oluwafemi Ogunmeru.

Jami'an Amoketun sun kama wani da tsabbar sabbin kudi N250,000 na bogi

A wani labarin, jami'an hukumar tsaro na kudu maso yamma wato Amotekun sun kama wani mutum, Celestine da takardun naira na bogi da adadin su ya kai N250,000.

Kara karanta wannan

Babban aiki: NDLEA ta kama 'yan kwaya 793 a Arewa, sun kwato kayan buguwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel