Kotu ta Daure Jagororin Jam’iyyar PDP a Kurkuku a Dalilin Cin N140m Saboda Murde Zabe

Kotu ta Daure Jagororin Jam’iyyar PDP a Kurkuku a Dalilin Cin N140m Saboda Murde Zabe

  • Babban kotun tarayya da ke Bauchi ya yankewa wasu jiga-jigan PDP shekaru biyu a gidan kaso
  • Alkali ya samu Sale Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya da karbar kudi saboda ayi magudi
  • Kotu ta ce a 2015 an ba ‘Yan siyasar N140m da nufin ayi murdiya a Bauchi a zaben shugaban kasa

Bauchi - Babban kotun tarayya mai zama a garin Bauchi, ya daure wasu jagorori na jam’iyyar hamayya a jihar a kan laifin badakalar satar miliyoyin kudi.

Gidan talabijin Channels ta rahoto Sale Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya za su yi zaman gidan gyaran halin shekaru biyu bayan samunsu da laifi.

Alkali ya samu wadannan ‘yan siyasa da aikata laifuffukan da suka shafi kutun-kutun da satar kudi har N142,460,000.00 kamar yadda EFCC ta bayyana.

A ranar Asabar Hukumar ta fitar da jawabi, ta bakin Kakakinta, Wilson Uwujeren, ta sanar da wannan nasara da ta samu a babban kotun tarayyan kasar.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Gwamnoni Ba Su Hakura ba, Za Su Sake Kai Karar Gwamnatin Buhari a Kotu

Hukuncin Alkali Hassan Dikko

The Cable ta ce Mai shari’a Hassan Dikko ya daure wadannan mutane biyu da aka tuhuma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Yunin 2018 aka fara gurfanar da Sale Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya a kotu, daga nan kuma aka cigaba da shari’ar a Oktoban 2018.

'Yan PDP
Taron magoya bayan PDP a 2015 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana zargin cewa Sale Gamawa da takwaransa Aminu Gadiya sun karbi fiye da Naira miliyan 142 domin murde zaben shugaban kasa a Bauchi tun a 2015.

A lokacin da aka karanto masu laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa, ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP sun musanya zargin, su ka nuna cewa su na da gaskiya.

Sale Gamawa, Aminu Gadiya sun shiga uku

Bayan shekaru kusan biyar ana shari’a a kotun tarayyar, Alkali ya ba hukumar EFCC gaskiya.

Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto, Alkali Dikko ya ce kudin da suka shiga hannun Gamawa da Gadiya, sun zarce abin da dokar kasa tayi tanadi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ya maye gurbin Shekarau a matsayin dan takarar sanatan NNPP

Ganin su na da iyali, Alkalin ya yi masu rangwame amma tare da yin ukubar da za ta zama darasi, ya ce su yi shekaru biyu a daure ko su biya Naira miliyan uku.

Siyasar amfani da addini

A baya kun samu labari cewa Shehu Sani ya fadi yadda ya taimakawa Musulmai a Giwa, Birnin Gwari, Jere, Rigasa a lokacin da yake majalisar dattawa na kasa.

Babban ‘Dan siyasar ya ce ‘Yan Siyasan Kaduna masu yaudara da tikitin Muslim Muslim su fadi ayyukan da suka yi wa al'ummar Musulmai da ke zama a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel