Zai Zama Abin Kunya Ga Gwamnonin Apc a Arewa Su Ci Dunduniyar Tinubu, Inji Gwamna Sule

Zai Zama Abin Kunya Ga Gwamnonin Apc a Arewa Su Ci Dunduniyar Tinubu, Inji Gwamna Sule

  • Gwamnan jihar Nasarawa ya bayyana kadan daga dalilan da suka sa APC ta ba dan takararta na shugaban kasa tikitin takara
  • Abdullahi Sule ya ce babu gwamnan APC a Arewa da ke adawa da tafiyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 na bana
  • Ya ce abin kunya ne ace wai akwai gwamnonin APC a Arewa na shirin cin dunduniyar dan takarar da suka aminta dashi

Najeriya - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce, babban abin kunya ne ga gwamnonin APC a Arewacin Najeriya su ci dunduniyar dan takararsu na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana gidan talabijin na Channels.

Ya kara da cewa, gwamnonin APC a Arewacin Najeriya sun fito a baya don bayyanawa balo-balo cewa, suna son mulki ya koma Kudu, don haka suka marawa Tinubu baya a zaben fidda gwani.

Kara karanta wannan

'APC Ta Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya Wanda Ka Iya Shafar Su Tinubu a 2023'

Abin kunya ne a ce gwamnonin APC na Arewa za su ci amanar Tinubu
Zai Zama Abin Kunya Ga Gwamnonin Apc a Arewa Su Ci Dunduniyar Tinubu, Inji Gwamna Sule | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ana yada jita-jita gwamnonin APC na shirin yaudarar Tinubu

Idan baku manta ba, ana yawan yada jita-jitan cewa, akwai lauje cikin nadi a APC, domin gwamnonin jam’iyyar a Arewa suna shirin marawa Atiku baya, Premium Times ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana, gwamna Sule ya ce:

“Na ji jita-jitan cewa wasu gwamnonin APC a Arewa basa yiwa Asiwaju Tinubu aiki. Zan yi matukar mamaki da kaduwa idan akwai wani gwamna.
“Idan za ka tuna, zai zama abin kunya ga gwamnonin APC a Arewa musamman a ce su juya mu ce ba sa son Asiwaju. Mutane ma za su mana dariya.
“Dalili kuwa shine lokacin da batun kujerar ya taso, gwamnonin APC a Arewa mun fito fili ba tare da boye-boye ba muka ce muna son kujerar nan ta bar Arewa ta koma Kudu.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

“Ta haka ne aka samar da Asiwaju. Don haka a ce wai wadannan gwamnonin da suka yi aiki tukuru kuma suka sa rayuwarsu a kan suna son mulkin karba-karba don yiwa kowa adalci a kasar a ce su ne kuma za su ci dunduniyar kai mulki Kudu (ba haka bane).
"Babu gwamnonin da ke hakan.”

A baya mun kawo muku rahoton da ke bayyana zarge-zargen wasu gwamnoni 11 da sanataoci da jiga-jigan siyasar da ke kokarin barin tsagin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel