"Gwamnoni 11 da Sanatocin Jam’iyyar APC 35 Suna Yi wa Atiku Aiki a Boye a Arewa"

"Gwamnoni 11 da Sanatocin Jam’iyyar APC 35 Suna Yi wa Atiku Aiki a Boye a Arewa"

  • Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa ya ce Jam’iyyar PDP za ta ci zabe
  • Daniel Bwala ya fadawa Duniya cewa a APC akwai Gwamnoni da Sanatocin masu yi masu aiki ta bayan fage
  • ‘Dan siyasar bai iya kawo sunayen Gwamnonin jihohi da ‘Yan majalisun APC da ke taimakon takaransu ba

Abuja - Daniel Bwala wanda yana cikin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa ya ce mai gidansa ya fi kowa damar lashe zaben 2023.

A ranar Juma’ar nan, 6 ga watan Junairu 2023, Vanguard ta rahoto Daniel Bwala yana cewa akwai wasu Gwamnoni da Sanatocin APC da ke tare da su.

Bwala ya ce a wasu jihohin Arewacin Najeriya, akwai gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dattawa da aka zaba a APC da su na goyon Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Gwamna ya fadi dalili 1 da yasa gwamnonin APC a Arewa ke son Tinubu

Mai magana da yawun bakin kwamitin takaran yake cewa wadannan ‘yan siyasa su na yi wa ‘dan takaran jam’iyyar PDP aiki ba tare da sun fito karara ba.

Bwala ya na hangen nasara

Wannan magana ta fito daga bakin Bwala ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise a game da zaben 2023 da mubaya’ar Olusegun Obasanjo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam’iyyar APC
Yakin neman zaben APC Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook
“Gwamnonin Arewa 11, sannan ina tunanin da Sanatoci 35 zuwa 37 su na yi wa Atiki aiki a boye.
Idan kun lura a wajen yakin neman zaben shugaban kasarsu, idan suka ce ‘Najeriya’, mutane za su amsa masu ne da cewa ‘Sai Atiku Abubakar!’.
Shiyasa a taron karshe da suka yi a Kano a ranar Laraba, suka daina cewa ‘Najeriya’, domin sun san taron mutanen za su amsa ne da kiran Atiku.

Kara karanta wannan

Gwamnonin da Ake Rigima da su a PDP Sun Hadu a Ibadan, An Samu Labarin Matsayarsu

Wanene da wanene ke goyon bayan PDP?

Da aka matsa masa ya fadi sunayen wadanda ke marawa Atiku baya a zaben bana, an rahoto ‘dan siyasar yana cewa ba a fallasa irin wadannan manyan sirri.

Bwala ya ce ko yaronsa mai shekara hudu da haihuwa, ya san ba a fitar da irin wadannan bayanai. Har zuwa yanzu dai an bar gaskiyar maganar a duhu.

Duk mun bi Tinubu - Gwamna

Sai dai rahoton ya ce wannan ikirari ya na da rauni domin Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya karyata maganar, ya ce suna tare da ‘dan takaransu.

Abdullahi Sule yake cewa gwamnonin APC sun marawa Asiwaju Bola Tinubu baya 100 bisa 100.

Chukwuma Soludo ya yabi Kwankwaso

Labari ya zo cewa Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne Dan takaran shugaban kasar na NNPP, ya busawa jam’iyya mai kayan marmari rai da ya je Anambra

A nan ne Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya yi wa tsohon Gwamnan na Kano da ‘yan tawagarsa fatan alheri a zaben shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel