Sauya Shekar Bindow Babban Rashi Ne Ga Jam'iyya Mai Mulki, Ribadu

Sauya Shekar Bindow Babban Rashi Ne Ga Jam'iyya Mai Mulki, Ribadu

  • Sakataren tsare-tsare na APC a Adamawa ya ce jam'iyyar ta yi babban kuskure na rasa tsohon gwamna Bindow
  • Mustapha Atiku Ribadu ya ce sauya shekar Jibrilla Bindow koma baya ne mai girma ga jam'iyyar APC
  • Tsohon gwamnan tare da magoya bayansa sun tabbatar da sauya sheƙa daga APC a hukumance, lamarin da baiwa wasu daɗi ba

Adamawa - Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, ya bayyana cewa sauya sheƙar tsohon gwamna, Jibrilla Bindow, babbar matsala ce ga APC.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ribadu ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai ranar Laraba a Yola, babban birnin jihar.

Jibrilla Bindow.
Sauya Shekar Bindow Babban Rashi Ne Ga Jam'iyya Mai Mulki, Ribadu Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa fitar Bindow ba rashi bane kaɗai, babban koma baya ne idan aka yi la'akari da ɗumbin magoya baya da masu fatan Alherin da tsohon gwamnan ke da su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar Gwamna a Arewa Ya Janye, Ya Koma Bayan Jam'iyar PDP

Sakataren ya yi bayanin cewa duk da Bindow ya yi kuskure a lokacin mulkinsa kasancewarsa ɗan adam, amma nasarorin da ya samu musamman a bangaren manyan ayyuka abin a yaba ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sauya sheƙar Bindow a lokacin da zaɓe yake gab da isowa abin damuwa ne kuma babban rashi ne ga jam'iyya. Duk da kuskuren Bindow zamu iya tuna abubuwa masu kyau da ya kawo jihar nan na ci gaba."
"Zamu ci gaba da ba shi girman da ya cancanta da shi a matsayin gwamnan APC na farko a jihar, wanda ya yi iya bakin kokarinsa wajen gyara Adamawa amma ya yi rashin nasara a zaɓe bayan samun kuri'u sama da 300,000."

- Mustapha Atiku Rubadu.

Duk da haka APC zata ci zaɓe - Ribadu

Sai dai duk da haka jigon siyasan ya bayyana cewa APC ce zata samu nasara a jihar Adamawa duk da wannan babban rashin kuma suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da nasara ga yan takara.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Punch ta rahoto Ribadu na cewa:

"Yayin da nake wa tsohon gwamnan mu fatan Alheri, ina ƙara jaddada cewa mun ɗauki dukkan matakin jurewa ficewar Bindow. Zamu ci gaba da aiki domin APC ta samu nasara tun daga sama har ƙasa."

A wani labarin kuma Rayuka Sun Salwanta Yayin da Mambobin PDP da APC Suka Kacame da Faɗa a Osun

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne a gaban Ɗan takarar Sanatan Osun ta yamma na APC, Amidu Tadese, da abokin hamayyarsa na PDP, Lere Oyewumi.

Manyan 'yan takaran biyu sun zabi lokacin gangamin kamfensu na Ikere a rana ɗaya, daga nan matsalar ta faro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel