Jerin Wayoyi 47 da Manhajar WhatsApp Za Ta Daina aikin kansu a 2023

Jerin Wayoyi 47 da Manhajar WhatsApp Za Ta Daina aikin kansu a 2023

  • Miliyoyin wayoyi a fadin duniya na gab da daina WhatsApp daga Junairun sabuwar shekara
  • Masu amfani da wadannan wayoyi da zasu daina aiki su shirya tanadar sabuwar waya tun da wuri
  • Manhajar WhatsApp ta shahara cikin al'umma inda kusan kowa na amfani da ita wajen hira
  • A cewar Wikipedia, sama da mutane bilyan 2 na amfani da WhatsApp a fadin duniya

Manhajar WhatsApp za ta daina aiki a wayoyi da dama nan da ranar 1 ga watan Junairu 2023.

A sakon da ta aikewa dimbin masu amfani da WhatsApp, ta bayyana cewa zasu daina amfani da manhajar kan wasu wayoyi guda 47.

A cewar jawabin, wayoyin Android da Iphone duka wannan zai shafa.

A shafin FAQ dinta, WhatsApp tace:

"Wayoyi da manhajoji kan canja akai-akai, saboda haka lokaci bayan lokaci mukan sake nazari kan manhajojinmu kuma muyi sauyi."

Kara karanta wannan

Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu

"Kamar sauran kamfanonin sadarwa, Muna zaben wayoyin da manhajarmu zata daina aiki akansu ne dubi ga tsufarsu da kuma karancin masu amfani da su."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wadannan wayoyi mafi akasari basu samun kariya, kuma karfinsu ya yi raunin da WhatsAPP ba zata iya aiki a kansu ba."
Whatspp
Jerin Wayoyi 47 da Manhajar WhatsApp Za Ta Daina aikin kansu a 2023
Asali: Facebook

Ga jerin wayoyin da WhatsApp zata daina aiki

iPhone 5

iPhone 5c

Archos 53 Platinum

Grand S Flex ZTE

Grand X Quad V987 ZTE

HTC Desire 500

Huawei Ascend D

Huawei Ascend D1

Huawei Ascend D2

Huawei Ascend G740

Huawei Ascend Mate

Huawei Ascend P1

Quad XL

Lenovo A820

LG Enact

LG Lucid 2

LG Optimus 4X HD

LG Optimus F3

LG Optimus F3Q

LG Optimus F5

LG Optimus F6

LG Optimus F7

LG Optimus L2 II

LG Optimus L3 II

LG Optimus L3 II Dual

LG Optimus L4 II

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Shiga Yin Gwanjo da Wasu Kadarorin Diezani Alison-Madukwe

LG Optimus L4 II Dual

LG Optimus L5

LG Optimus L5 Dual

LG Optimus L5 II

LG Optimus L7

LG Optimus L7 II

LG Optimus L7 II Dual

LG Optimus Nitro HD

Memo ZTE V956

Samsung Galaxy Ace 2

Samsung Galaxy Core

Samsung Galaxy S2

Samsung Galaxy S3 mini

Samsung Galaxy Trend II

Samsung Galaxy Trend Lite

Samsung Galaxy Xcover 2

Sony Xperia Arc S

Sony Xperia miro

Sony Xperia Neo L

Wiko Cink Five

Wiko Darknight ZT

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida