Matashi Ya Koka Bayan Budurwa Ta Shekaru 3 Ta Auri Wani Da Kudinsa, Ya Wallafa Hirarsu

Matashi Ya Koka Bayan Budurwa Ta Shekaru 3 Ta Auri Wani Da Kudinsa, Ya Wallafa Hirarsu

  • Wani matashi dan Najeriya ya hadu da sharrin soyayya bayan budurwarsa ta shekaru uku ta auri wani daban
  • Abun da ya fi masa ciwo shine cewa ta yi masa karya cewa yar'uwarta za ta yi aure sannan ta sanya shi kashe kudadensa
  • Ya kaita siyayya a ranar Talata sannan a ranar Laraba ya gano cewa za ta yi aure a ranar Asabar na wannan makon

Wani matashi dan Najeriya wanda aka yaudara yana tunanin kawo karshen komai bayan budurwar da ya shafe shekaru uku yana soyayya da ita ta ci amanarsa.

Mawallafi Maazi Ogbonnaya Okoro ya wallafa hirar mutumin na Whatsapp a Facebook inda ya bayyana ainahin abun da ya faru.

Matashi da sakonni
Matashi Ya Koka Bayan Budurwa Ta Shekaru 3 Ta Auri Wani Da Kudinsa, Ya Wallafa Hirarsu Hoto: Ivan Pantic, Facebook/Maazi Ogbonnaya Okoro II
Asali: Getty Images

Da yake martani ga hirar, Ogbonnaya ya nuna fushinsa kan abun da matashiyar ta aikata, yana mai cewa babu wanda ya cancanci irin haka imma namiji ko mace.

Chindera ta yi wasa da hankalinsa sosai

A hirar tasu, mutumin ya ce budurwarsa mai suna Chidera ta fada masa cewa yar'uwarta zata yi aure. Sai saurayin ya dauki budurwar tasa ya je ya yi mata siyayya a kasuwar Onitsha a ranar Talata da Laraba don shirya ma bikin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya kasance ne don budurwar ta fada masa cewa a ranar Juma'a za a yi bikin al'ada sannan a ranar Asabar a daura aure.

Bayan ya mata siyayya, ya kuma aikewa yar'uwar budurwar N50k sannan ya saka ta a mota don komawa gida a ranar Alhamis. Kawai sai ya gano cewa budurwar tasa ce zata yi aure.

Jama'a sun yi martani

Eziamaka Mma Okoye ya ce:

"Allah ya kyauta amma dai wannan jinsi nawa na da karfin hali faaa, ka dau hakuri dan uwana nima jinsinka na wahalar da ni da wasu mata masu soyayya ta gaskiya. a karshe duk za mu ji daidai."

Nancy Ijeoma Silver ta ce:

"Shekaru uku kacal, kawata wacce saurayin da suka shafe shekaru 9 suna soyayya ya yaudareta kuma ta ce me.
"Gaye ya auri budurwar da ya gabatar gaban kawata a matsayin abokiya kawai.
"Mallam dole rayuwa ta ci gaba, dukkanin jinsin ba nunawa junansu bakin hali. Ya kakkabe kansa sannan ya ci gaba da rayuwa."

Amarya ta biya kudin sadakin aurenta da kanta

A wani labarin kuma, mun ji cewa ta amarya ta rufe ido ta ciro kudi daga aljihunta domin biyan sadakin aurenta.

matashiyar mai shekaru 34 ta ce ta yi hakan ne ganin cewa ta fi angon nata nauyin aljihu domin digiri gare ta har guda uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel