Farashin Tikitin Jirgin Kasan Abj-Kd Yayi Tashin Gwauron Zabi

Farashin Tikitin Jirgin Kasan Abj-Kd Yayi Tashin Gwauron Zabi

  • Kaiwa da kawowar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna sun dawo a ranar Litinin inda NRC ta tayar da kudin tikitin kowanne tarago
  • A taragon ya-ku- Nayi, an kara kudi har N1000 a kan farashin baya yayin da aka kara N1500 a na matsakaita wato na kasuwa, sai na muhimman mutane aka kara N3000
  • Karakainar jiragen kasan ta dawo da sabon salo inda gwamnati ta kara inganta tsaro yayin da ake siyar tikitin da wasu muhimman bayanan fasinja

Abuja - A yayin da karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna ta dawo bayan watanni takwas da dakatawarta, farashin yayin tashin gwauron zabi na kowanne rukunin fasinjoji, Daily Trust ta rahoto.

Farashin tikiti
Farashin Tikitin Jirgin Kasan Abj-Kd Yayi Tashin Gwauron Zabi. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Idan za a tuna, ministan sufuri, Alhaji Muazu Sambo Jaji ya sanar a makon jiya cewa jiragen zasu koma aiki a wannan makon kuma matafiya dole su shirya fuskantar tashin farashin kudin kujera.

Kara karanta wannan

Rikici: Makiyaya da manoma sun yi fada, an kashe mutum 8 har da yada, an kone gidaje 47 a jihar Arewa

Duk da ba a sanar da kudin kujerun kowanne rukuni ba, masu aiki a wurin sun tabbatar da cewa an saka sabon farashin tikitin kuma Legit.ng Hausa ta duba manhajar tare da tabbatarwa.

Bayani kan sabon farashin tikiti ya bayyana cewa, taragon Economy wanda a baya ake siyar da tikitinsa kan N2600 yanzu ya koma N3600 wanda ke bayyana karin N1000 kan sabon farashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tarago na ‘yan kasuwa kuwa, a halin yanzu ana siyar da tikitin kan N6500 a maimakon a baya da ake siyar da shi kan N5000, karin N1500 a kai.

Shi kuwa taragon mutane na musamman a baya ana siyar da tikitinshi kan N6,000 amma a halin yanzu ya koma N9000, karin N3000 a kan farashin baya.

Idan za a tuna, a yayin da annobar korona ta kunno kai, NRC ta tada kudaden tikitin da kashi 100.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Legit.ng Hausa ta zanta da fasinja

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani fasinja wanda ya hau jirgin safe mai suna Muhammad Musa, ya sanar da cewa a tsorace ya hau duk da yafi tsoron bin hanyar Abuja ta mota fiye da jirgin kasa.

”A gaskiya akwai jami’an tsaro sosai. A Rigasa na hau jirgin kuma an tabbatar da cewa in har babu NIN, toh babu shiga jirgin kasan.
”Amma kuma yawan yadda jama’a suka saba tururuwar zuwa hawan jirgin kasan ba haka suka zo yau ba. Ni dai tsam nayi da zuciyata kuma nazo na hau.”

FG ta sanar da ranar dawo da karakainar jiragen kasan Abuja zuwa Kaduna

A wani labari na daban, Ministan sufuri, Muazu Sambo, yace za a dawo jigilar fasinjojin Abuja zuwa Kaduna a jirgin amsa zuwa karshen watan Nuwamba.

Duk da ministan bai bayyana wacce rana ba, yace nan babu dadewa hakan zata faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng