An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Otel Sati Ɗaya Bayan Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta

An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Otel Sati Ɗaya Bayan Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta

  • Rundunar yan sanda na Jihar Benue ta tabbatar da cewa an tsinci gawar wata Takor Veronica a dakin otel a unguwar Nyinma
  • Yan sanda sun ce an tarar da gawarta da tufafi kuma babu alamun rauni a jikinta wadda hakan na nuna akwai yiwuwar ba kashe ta aka yi ba
  • Kakakin yan sandan Benue, Cathrene Anene ta ce a halin yanzu an kama mutum uku da ake zargi da hannu a mutuwar amma likitoci za su yi karin haske

Jihar Benue - An tsinci gawar Jaruma Takor Veronica a cikin wani daki na Otel a Jihar Benue, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar rahotanni daban-daban, an gano gawar na Veronica ne kimanin sati baya bayan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta.

Kara karanta wannan

Sai ka kawo mahaifinka ko Malam Liman: Kotu ta ba da sharadin beli ga wanda ya kira Ganduje dan rashawa

Da Ɗuminsa: An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Hotel
An Tsinci Gawar Jarumar Fim Ta Najeriya a Ɗakin Hotel a Benue. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto cewa an tsinci gawarta ne a wani dakin otel a unguwar Nyinma na Makurdi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene ta tabbatar da afkuwar lamarin.

An kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisar jarumar, Anene

Kakakin yan sandan ta ce an kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a mutuwar jarumar.

"An kawo rahoton mutuwar wata mata a otel amma muna jiran bayani daga likitoci. Ba mu ga alamun rauni a jikinta ba. Don haka gwajin likitoci zai sanar da mu sanadin mutuwarta. Matar da ta mutu tana sanye da tufafi; ba mu ga alamar rauni a jikinta ba.
"An kama mutane uku da ake zargi da hannu a wannan, za su bamu karin bayani. Ba za mu iya cewa kashe ta aka yi ba domin ba mu ga alamar rauni ba," in ji ta.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Tsageru sun kone rugar makiyaya kurmus a yankin Kudancin Kaduna

Abokanta da abokan aiki sun yi ta wallafa sakon ta'aziyya a dandalin sada zumunta.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel