Yanzu-Yanzu: Kirstocin Arewa Sun Yanke Shawarar Atiku Zasu Marawa Baya - Dogara

Yanzu-Yanzu: Kirstocin Arewa Sun Yanke Shawarar Atiku Zasu Marawa Baya - Dogara

Dogara
Yanzu-Yanzu: Dogara Yace Sun Marawa Atiku Baya A Zaben 2023 Hoto: The Punch
Asali: UGC

Tsohon shugaban majalissar tarayya Hon. Yakubu Dogara yace basu da wata mafita face su marawa dan takarar jami'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar baya a zaben 2023.

Dogaran Wanda na gaba-gaba wajen ganin baikon jam'iyyar APC na fitar da dan takarar shugaban kasa musulmi kuma mataimakin sa ma musulmi.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa Dogara ya yanke hukunce bayan da aka samu sabani tsakanin sa da tsohon sakataran gwamnatin tarayya Babbachir Lawan wanda shima ke kin lamirin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar ta amince da Abubakar ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a Abuja, bayan amincewa da rahoton kwamitinta na tuntuba simon Achuba, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi ne ya gabatar da rahoton.  Kungiyar ta ce bayan tantance dukkan 'yan takarar shugaban kasa, ta gamsu Abubakar shine mafi dacewa. “A bayyane yake cewa jam’iyyar APC na shirin yiwa dimokuraɗiyya kaca-kaca don haka ba za mu iya mara mata baya ba. sannan jam’iyyar a yanzu ta ki amincewa da rungumar dunkulewar kasa gabannin zaben 2023,” in ji Simon Yayin da yake magana game da sauran yan takarar jam'iyyar NNPP da LP yace: "Za su iya fitowa a nan gaba, amma mu dai daga dukkan alamu, PDP ce zata zama mana mafi wanda ya kamata mu marawa baya" “Abin da kawai ake bukata shi ne a magance wasu matsaloli da kalubalen da kasar nan ke fuskanta." Dogara ya kuma gabatar da wani rahotan wanda yace shi ne muryar ‘yan kungiyar da suka amince da shi gaba daya. Kungiyar ta kara da cewa za ta tattauna batun daukar Abubakar da PDP domin samun “tabbacin da ya wajaba daga jam’iyyar (PDP) don tafiyar da gwamnati”. Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki bayan Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ya amince da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP). ‘Yan kungiyar Kiristocin Arewa a jam’iyyar APC karkashin jagorancin Lawal, sun nisanta kansu daga batun marawa dan takarar LP baya kuma saka ce tsohon Lawan din ya yi magana da akan kansa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel