Yadda Matar Aure Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Ya Mutu Yayin Da Ya Kusance Ta Don Ƙoƙarin Neman Hakkinsa Na Aure

Yadda Matar Aure Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Ya Mutu Yayin Da Ya Kusance Ta Don Ƙoƙarin Neman Hakkinsa Na Aure

  • Wata matar aure ta halaka mijinta a garin Oyo a yayin da ya ke neman ta bashi hakkinsa na aure
  • Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, Olamilekan Salaideen, ya shafe kimanin wata uku ba ya tare da matarsa
  • A ranar da abin ya faru, sun dawo gida bayan an sulhunta su ya nemi ya kusance ta kuma ta ki yarda, suka fara rikici sai ta caka masa wuka a kirji

Jihar Oyo - An rahoto cewa wani mutum mai suna Olamilekan Salaideen, ya mutu bayan matarsa mai shekara 27, Odunayo, da caka masa wuka a gidansa da ke Oko Oba, birnin Oyo, jihar Oyo, rahoton The Guardian.

Punch Metro ta tattaro cewa Odunayo ta aikata laifin ne yayin da mijinta ya yi yunkurin kwanciyar aure da ita.

Wacce ake zargi
Yadda Matar Aure Ta Caka Wa Mijinta Wuka Ya Mutu Yayin Da Ya Ke Kokarin Neman Hakkinsa Na Aure Daga Gare Ta. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke holen Odunayo tare da wasu wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban su 25, mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Adewake Osifeso, ya ce Odunayo wanda ba da dadewa ba aka sulhunta ta da mijinta ta halaka shi ne yayin da ya ke kokarin kwanciya da ita.

Yadda matar auren ta caka wa mijinta wuka yayin da ya nemi ya kusance ta don kwanciyar aure

Osifeso ya ce:

"A ranar 17 ga watan Nuwamban 2022, wani Ismaila Tijani ya kai rahoto a hedkwatar rundunar yan sanda ta Durbar cewa, Odunayo, matar dansa Olamilekan Salaideen, dan shekara 35, ta caka masa wuka ya mutu.
"Binciken farko da aka yi ya nuna matar da marigayin sun dawo gidansu a Oko Oba, garin Oyo, a ranar da abin ya faru bayan wata uku ba su tare. Marigayin ya nemi hakkinsa na aure amma matar ta ki yarda.

"Hakan ya janyo suka yi kokawa kuma marigayin ya kwace wayar matarsa ya rangada shi a kasa. A martaninta, matar da caka wa marigayin wuka a kirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa."

Wacce ake zargin ta amsa laifinta da rawar da ta taka a mumunan lamarin, ya kara da cewa za a gurfanar da ita a kotu da zarar an kammala bincike.

Matar Aure Ta Halaka Mijinta Ta Hanyar Daba Masa Wuka a Adamawa

A wani labari mai kama da wannan, yan sanda a jihar Adamawa a ranar Juma’a, 22 ga watan Yulin 2022, sun kama wata matar aure mai shekaru 20 kan zargin caka wa mijinta mai shekaru 38 wuka tare da sanadin mutuwarsa.

DSP Suleiman Nguroje, kakakin yan sandan jihar ya ce rigima ya shiga tsakanin wacce ake zargin mai suna Caroline Barka, mai zaune a Unguwan Tamiya, karamar hukumar Madagali, da mijinta, Barka Dauda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel