Sojoji Sun Kame Abokan Harkallar ’Yan Bindiga 5 Dauke da Kudi N19.5m a Katsina

Sojoji Sun Kame Abokan Harkallar ’Yan Bindiga 5 Dauke da Kudi N19.5m a Katsina

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana ayyukan da jami'anta suka yi a cikin makwanni biyu kacal na karshen watan Nuwamba
  • An kama wasu abokan harkallar 'yan bindiga a jihar Katsina dauke da makudan kudade, inji rahoton na sojoji
  • Hakazalika, a wasu ayyukan da aka yi an kamo wasu 'yan ta'adda a bangarori daban-daban na kasar nan baya ga hallaka wasu

FCT, Abuja - Jami'an sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kame wasu abokan harkallar 'yan bindiga a kauyen Daudawa da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina dauke da makudan kudi N19.5m.

Daraktan yada labarai na gidan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, PM News ta ruwaito.

Danmdani ya ce, an kama tsagerun ne a ranar 17 ga watan Nuwamba yayin da rundunar ke aikin bincike, inda yace an kuma kwato abin hawa da kuma wayoyin hannu biyar daga hannun wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Babban Jihar Arewa Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Wanda Ya Cancanta Su Zaɓa Shugaban Kasa A 2023

Ya bayyana cewa, an kuma hallaka wasu 'yan bindiga uku a kauyen Yambuki a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a ranar 20 ga watan Nuwamba, wasu kuwa sun tsere da raunuka.

Sojoji sun kama abokan harkallar 'yan bindiga
Sojoji Sun Kame Abokan Harkallar ’Yan Bindiga 5 Dauke da Kudi N19.5m a Katsina | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya bayyana adadin makamai da aka kwato da suka hada da bindigogi AK47 da alburusai da dama, Ripples Nigeria ta tattaro.

A bangare guda, ya ce an kamo wani da ake zargin dillalin makamai ne dauke da makamai da alburusa a hanyarsa ta zuwa Damari a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara daga Zaria.

Yadda aka fatattaki maboyar kasugumin dan bindiga

A wani bangaren, ya ce an yi kaca-kaca da maboyar kasurgumin dan bindiga, Malam Ila a kauyen Manawa na karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

A ranar 28 ga watan Nuwamba, sojoji sun kama wani dillalin makamai dauke da bindigogi AK47 guda biyar a boye cikin jaka a Gidan Ado na karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

Kara karanta wannan

‘Yan Ta’addan Sun Kone Ofishin INEC, Kayayyaki Masu Muhimmanci Sun Kone

Ya kuma bayyana cewa, wata rundunar ta yi nasarar kama 'yan ta'adda Kwazaye, Shelena da Ukande na karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

A cewarsa, an ce 'yan ta'addan da aka kamo sojoji ne na wani kasurgumin dan bindiga, Iorkoso Tyopaha da ke barna a kauyen Kaamne na jihar ta Benue.

Bayanansa sun bayyana nasarorin da rundunar sojin ta samu cikin mmakwanni biyu kacal na karshen watan Nuwamba.

A makon da ya gabata ne 'yan bindiga suka fatattaki jama'a a wani yankin jihar Zamfara, sun raunata mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel