'Yahoo Boy' Dan Shekara 27 Ya Kashe Budurwarsa, Idowu Buhari Da Duka A Ogun, Ya Bayyana Dalili

'Yahoo Boy' Dan Shekara 27 Ya Kashe Budurwarsa, Idowu Buhari Da Duka A Ogun, Ya Bayyana Dalili

  • Yan sanda sun kama wani matashi dan damfara intanet kan halaka buduwarsa mai suna Idowu Buhari
  • Wanda ake zargin, Obeta John ya fada wa yan sanda cewa an tura kudinsa zuwa asusun bankinta ne amma ta ki bashi
  • Kwamishinan yan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole ya bada umurnin a tura wanda ake zargin sashin SCID don zurfafa bincike

Jihar Ogun - Jami'an yan sandan jihar Ogun sun kama wani da ake zargin dan damfarar intanet ne, wato Yahoo Boy, Obeta John, kan kashe budurwarsa mai suna Idowu Buhari.

Marigayiyar dalibai ce da ke aji na farko a Gateway Polytechnic, Saapade, jihar Ogun a tsangayar karanta aikin jarida, Daily Trust ta rahoto.

Dan Yahoo
'Yahoo Boy' Dan Shekara 27 Ya Kashe Budurwarsa Da Duka A Ogun. Hoto: PM News
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wani Dalibi Kamaludeen Dan Shekera 22 Ya Caka Wa Abokinsa, Usman, Wuka Har Lahira A Bauchi

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya fada wa manema labarai a Abeokuta cewa an kama wanda ake zargin ne bayan an samu kiran neman dauki a hedkwatar yan sanda ta Ode-Remo.

A cewarsa, an sanar da yan sandan cewa wanda ake zargin da ke zaune a No 3 Mojubade, Eredu Ishara, ya rufe kansa da budurwarsa a daki, yayin da ya ke dukanta, PM News ta rahoto.

Oyeyemi ya ce wanda ake zargin ya yi wa budurwar duka kuma ta buga kanta a bango, anyi kokarin ya bude kofa amma ya ki.

Ya ce:

"Bayan samun kiran neman daukin, DPO na Ode-remo, CSP Fasogbon Olayemi ya taho da mutanensa inda suka tarar da wanda abin ya faru da ita kwance cikin jini bayan sun balle kofar.
"An garzaya da ita zuwa asibitin State House Ishara, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar ta mutu. Nan take aka kama wanda ake zargin, dan asalin jihar Enugu."

Kara karanta wannan

Ko Me Ya Yi Zafi? Ɗan Najeriya Ya Yi Wa Budurwarsa Yankar Rago a Kasar Waje

Dalilin da yasa saurayin ya kashe budurwarsa

Oyeyemi ya ce yayin masa tambayoyi, wanda ake zargin wanda ya amsa cewa

"Shi 'yahoo boy' ne, kuma wani ya biya shi kudi ta asusun bankin budurwarsa amma ta ki ba shi kudin.
"Ya cigaba da cewa jayayya kan kudin suke yi har suka fara fada kuma ya yi sanadin mutuwar ta."

Kwamishinan yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bada umurnin a kai wanda ake zargin sashin SCID domin zurfafa bincike.

Wani dan shekara 51 ya kashe matarsa da duka har Lahira a Ogun

Jami'an yan sanda sun kama wani magidanci mai suna Oluranti Badeko, kan zarginsa da halaka matarsa mai shekara 40, Folashade Badejo a jihar Ogun.

Daily Trust ta rahoto cewa abin ya faru ne a Orimerunmu a kauyen Mowe, a karamar hukumar Obafemi-Owode.

Asali: Legit.ng

Online view pixel