Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Babban Hadimin Gwamnan APC, Sun Nemi Fansa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Babban Hadimin Gwamnan APC, Sun Nemi Fansa

  • 'Yan bindiga sun je har gida, sun yi garkuwa da tsohon babban hadimin gwamnan jihar Ondo, Richard Omosehin
  • Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun kira matar mutumin, sun nemi a tattara musu miliyan N100m a matsayin fansa
  • Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, tace tuni ta fara kokarin ceto jigon APC cikin ƙoshin lafiya

Ondo - Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da, Mista Richard Omosehin, tsohon babban mai taimakawa gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a gidansa da ke Igbekebo, ƙaramar hukumar Ese Odo.

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Ondo ta tabbatar da garkuwa da mutumin, tace jami'ai sun baza komarsu yayin da ake kan bincike kan lamarin.

Harin 'yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Babban Hadimin Gwamnan APC, Sun Nemi Fansa Hoto: vanguard
Asali: Depositphotos

Wata majiya daga cikin iyalan mutun ta shaida wa jaridar Vanguard cewa tsohon hadimin gwamnan ya shiga hannun masu garkuwa da mutane ne ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Tinubi Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

A cewar mutunin, "Richard, babban jagora a jam'iyyar APC, mutane shida ɗauke da bindigu ne suka sace shi, waɗanda suka zo a Jirgin ruwa mai gudu kuma suka zarce gidansa suka tasa shi zuwa Jirgin kana suka tsere."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Lamarin ya auku da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar daren ranar Asabar. Mutane sun yi saurin sanar da 'yan sanda amma lokacin da suka ƙariso maharan sun riga sun tafi da mutumin."

Shin maharan sun nemi kuɗin fansa?

Basaraken garin Igbekebo, Oba Simon Dabo, yace, "Masu garkuwan sun bar mutumin ya kira matarsa a wayar salula kuma sun nemi miliyan N100m a matsayin kuɗin fansa."

Da aka nemi jin ta bakinsa, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar, Funmi Odunlami, yace dakaru na kan kokarin ceto mutunin cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Fitaccen Malami a Jihar Arewa, Sun Nemi Fansa

A ruwayar The Nation, Odunlami yace, "Mun riga mun fara kokarin kubutar da wanda aka sace kuma mun fara gudanar da bincike."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fitaccen matashin Malami a jihar Kwara tare da ɗan uwansa da ɗansa

Mahaifinsa wanda babban Malami ne da ake ganin girmansa a yankin ya yi kira ga hukumomi da mutane masu fatan Alheri su taimaka wajen kubutar da 'ya'yansa da jikansa.

Hukumar yan sanda reshen jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace jami'ai na kan aiki kuma sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel