Kalaman Minista Sun Jawo ‘Yan Majalisa Sun Bukaci Shugaban kasa Ya Tsige ta

Kalaman Minista Sun Jawo ‘Yan Majalisa Sun Bukaci Shugaban kasa Ya Tsige ta

  • ‘Yan majalisan da suka fito daga jihohin Neja-Delta sun sa kafar wando daya da Ministar tarayya
  • Ana zargin Sadiya Umar Farouq da nuna son kai a kan batun ambaliyar ruwan da aka yi a wasu jihohi
  • Sadiya Umar Farouq tace ambaliyar ta fi tasiri a Jigawa, wannan ya fusata wakilan Neja-Deltan

Abuja - Wakilan Neja-Delta a majalisar wakilan tarayya sun yi kira ga Mai girma Muhammadu Buhari da ya tsige Ministarsa, Sadiya Umar Farouq.

Premium Times tace ‘yan majalisar wakilan tarayyan sun nemi a tunbuke Sadiya Umar Farouq ne saboda kalaman da tayi a game da ambaliyar ruwa.

Kwanakin baya aka ji Ministar tana cewa Jigawa ce jihar da ta fi kowace gamuwa da masifa a sakamakon ambaliyar da aka yi a daminar shekarar nan.

‘Yan majalisar sun yi wannan kira yayin da suka zanta da 'yan jarida a ranar Litinin a Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Ina aka baro jihar Bayelsa fa?

Sadiya Umar Farouq ce Ministar jin-kai, bada agaji, da tallafin gaggawa a Najeriya. ‘Yan majalisa sun fusata da yadda tayi watsi da lamarin jihar Bayelsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministar ta fito tana cewa Bayelsa ba ta cikin sahun jihohi goma na farko da ambaliya tayi wa illa, hakan bai yi wa wakilan wannan yanki dadi ba.

Sadiya Umar Farouq
Sadiya Umar Farouq a taron FEC Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Rahoton yace annobar da aka yi a shekarar bana ta shafi wasu garuruwan da ke jihohi irinsu Benuwai, Kogi, Jigawa, Ribas, Bayelsa, Delta da Kano.

Mu na tir da Minista - Hon. Agbedi

Hon. Fred Agbedi wanda ya yi magana a madadin sauran abokan aikinsa, yace ‘yan majalisa sun yi Allah-wadai da yadda Minista ta siyasantar da masifar.

The Cable ta rahoto ‘yan majalisar su na kira ga Ministar jin-kan kasar ta yi murabus, idan kuwa ba haka ba, shugaban kasa ya karbe nauyin da ya damka mata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Fitaccen dan takarar majalisar wakilai a APC ya yi hadari, ya rasu

Fred Agbedi mai wakiltar Delta yace idan shugaban kasa bai tsige Ministar ba, za su dauki mataki, sai dai a jawabinsa, ba a ji matakin da suke shirin dauka ba.

Hon. Bob Solomon yace su na neman a sauke Ministar ne saboda irin abubuwan da take yi tun da ta shiga ofis, ba saboda kalamanta a game da ambaliya ba.

Siyasar Zamfara

Dazu labari ya zo cewa Kabiru Garba Marafa ya yi wa Bola Ahmed Tinubu albishir tun yanzu cewa ya ci zabe a jihar Zamfara domin bai da 'yan hamayya.

Da ake kaddamar da takarar APC, shugaban kwamitin kamfen yace babu wanda zai iya yi wa jam’iyya mai mulki adawa a kaf Zamfara, sai dai a wata jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel