Rai Bakin Duniya: Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yace ga Garinku

Rai Bakin Duniya: Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yace ga Garinku

  • Matashi Shehu Lili Kofar Atiku yace ga garinku kasa da sa’o’i 24 da daura aurensa da masoyiyarsa a jihar Sokoto dake arewacin Najeriya
  • An gano cewa Shehu yayi ciwon Maleriya a watan Satumba kuma ya sha magani inda ya warke har aka daura aurensa a Lahadi da ta gabata
  • Shamsu abokin Shehu, yace abokinsa ya fito daga gida ranar Litinin inda suka gaisa amma sai ciwon ya taso masa, a take ya fadi ya rasu

Sokoto - Wani matashi mai suna Shehu Lili dake yankin Kofar Atiku ya rasa ransa kasa da sa’o’i 24 bayan daurin aurensa da masoyiyarsa a jihar Sokoto.

Shehu Lili
Rai Bakin Duniya: Kasa da Awa 24 da Daura Aurensa, Ango Yace ga Garinku. Hoto daga Shamsu Buratai
Asali: Facebook

Wani ‘dan uwan iyalan, Shamsudeen Buratai wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace Lili ya rasu ne bayan rashin lafiyar farat daya, shafin LIB suka rahoto.

Kara karanta wannan

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

Kamar yadda Buratai yace, an daura auren angon wurin karfe 5 na yammacin Lahadi, 30 ga watan Oktoban 2022 a kofar Atiku dake Sokoto kuma yace ga garinku da safiyar Litinin.

“Shehu abokina ne tun muna yara kuma abokai gidajenmu suke sama da shekaru 30. Ya samu cutar zazzabin cizon sauro ne wacce ke kayar da shi duk sanyi. Kamar kowacce shekara, ciwon ya taso shekarar nan wurin Satumba wanda ya sha magani kuma ya samu lafiya.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Yace.

“A safiyar yau wurin karfe 9 na safe Shehu ya fito kuma ya same su har muka gaisa. Babu dadewa sai ya fara jin wani iri kuma yace mana ya tsammanin cutar da ce take son dawowa. Abu na gaba shi ne faruwar Shehu wanda daga nan kuma bai tashi ba.”

- Shamsu yace.

Tuni dai aka birni marigayin angon kamar yadda addini ya tanadar.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina

A wani labari na daban, wata budurwa a ake shirin daurawa aure, Fatima Hassan Fari ta rasu a ranar da za a daura mata aure a karamar hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa Fatima ta rasu ne misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar 2 ga watan Janairun 2021, awanni uku kafin daura mata aure da aka yi shirin yi karfe 10 na safe.

An yi mata jana'iza misalin karfe 2 na ranar Asabar din bisa koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel