Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa

Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa

  • Rundunar sojojin kasan Najeriya ta fitar da wasu lambobin da ‘yan kasa zasu yi wa kira gaggawa idan wata barazanar tsaro ta faru a kasar
  • Rundunar tayi kira ga ‘yan Najeriya da su hanzarta kira kai tsaye, aika sakon kar ta kwana ko sakon WhatsApp domin kai rahoton abinda ke faruwa
  • Lambobin suna zuwa ne bayan kwanaki kadan da rundunar ‘yan sanda ta fitar da tasu kuma Buhari yayi kira da a kwantar da hankali

FCT, Abuja - Rundunar sojin kasan Najeriya, ta bada lambobi na musamman ga ‘yan kasa domin rahoto tare da kai bayanai kan duk wata barazanar tsaro.

Sojoji
Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Rundunar sojin kasan ta Najeriya ta wallafa lambobin ne a shafinta na soshiyal midiya a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Hari a Abuja: Buhari ya ba 'yan Najeriya shawari bisa gargadin da Amurka suke kan Abuja

A cikin makonni biyu da suka gabata, tsoro da damuwa sun cika zukatan jama’a bayan wasu kasashen ketare sun bada shawarwari kan barazanar kai farmakin ‘yan ta’adda a wasu sassan kasar nan.

Amurka da Ingila sun ja kunnen jama’arsu kan yuwuwar kai farmaki Najeriya balle babban birnin tarayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda sakon da Rundunar sojin kasan ta fitar, tace ‘yan kasa ta wadannan lambobin na musamman zasu iya bada rahoto da zai taimaki sojojin wurin shawo kan rashin tsaro.

“Ku kai rahoton duk wasu bayanai da zasu taimaki sojojin wurin yaki da rashin tsaro ta hanyar kiran waya, sakon kar ta kwana ko sakon WhatsApp ga wadannan lambobin.
“Ana kira ga ‘yan masa da su latsa wadannan lambobin 193 ko su kira wadannan na gaggawan:
07017222225, 09060005290,08099900131, 08077444303.

A daya bangaren, shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan Najeriya da kada su tashi hankulansu kan bayanan Amurka da Ingila inda ya kara da cewa jami’an tsaro sun aiki wurin kawar da barazanar tsaron da tabbatar da lumanar kowanne ‘dan kasa.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

A kwantar da hankali kuma a kai rahoto idan bayanai sun samu

Legit.ng Hausa ta samu zantawa da wata majiyar tsaro daga dakarun sojin sama dake aiki a Abuja, kuma ta bukaci a boye sunanta saboda bata da hurumin fitowa tayi magana kan barazanar tsaron.

Majiyar tace duk wannan tada hankulan da jama’a ke yi bai dace ba, kawai suna yin shi ne saboda tsabar tsoron da suka shiga amma ba fa wani abun tada hankali bane ke faruwa.

”Rundunar sojin kasa ta saki lambobin nan na koda ta baci ne saboda hankalin jama’a ya kwanta kuma ko da za a samu wani lamarin gaggawa.
”Tabbas akwai barazanar tsaro a babban birnin tarayya amma bai kai yanda jama’a suke ta daga hankalinsu babu dalili ba.
”Yanda ofishin jakadancin Amurka ne suka fitar da sanarwar yasa mutane ke tsammanin babbar matsala ce a kasa, amma fa ba wata babbar matsala bace. A kwantar da hankali kuma a kai rahoto a duk lokacin da aka samu bayanai.”

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro: IGP Alkali Baba Ya Fitar da Lambobin Kiran Gaggawa ga ‘Yan Najeriya

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

A wani labari na daban, a farkon makon nan ne ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi kan yuwuwar farmaki a babban birnin tarayya na Abuja.

Bayan ofishin jakadancin ya bayar da sanarwa, hukumar Birtaniya ta bayar da shawarin kai da kawowa ga ma’aikatan ta yayin da take sanar da raguwar ayyukanta.

Hakazalika, sauran kasashen Turai kamar su Ingila, Australia, Jamus, Bulgaria, Ireland da Denmark duk sun sanar da rage ayyukansu yayin da zasu dinga mayar da hankali kan na dole a Najeriya.

Daily Trust ta gano daga majiyoyin diflomasiyya cewa, sauran kasashen sun bi sahun Amurka ne bayan jerin taruka, yada bayanan sirri da kuma gamsassun shaidu kan hatsarin dake tattare da birnin tarayyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel