Tikitin Musulmi Da Musulmi: APC tace Da Alamun Yakubu Dogara Ya Fara Samun Tabuwan Hankali

Tikitin Musulmi Da Musulmi: APC tace Da Alamun Yakubu Dogara Ya Fara Samun Tabuwan Hankali

  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya caccaki tsohon kakakin majalisar wakilai
  • A cewar kwamitin Yakubu Dogara, ya ƙufula ne sabida yadda burinsa bai cika ba na zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
  • An zargi tsohon kakakin da ƙin jagorantar yakin neman zabe da nuna kyama ga jam’iyya, da amafani da addini dan yaƙarta

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi wasu kalamai ga tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

A cewar kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da sa hannun Bayo Onanagu, daraktan yaɗa labarai na kwamitin, yace da alama Yakubu Dogara ya ƙulufa tare da yanke ƙauna.

Kwamitin ya zargi Dogara da daukar nauyin munanan kalamai da ɓatanci kan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu kan rashin zaben sa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

Dogara
Tikitin Musulmi Da Musulmi: APC tace Da Alamun Yakubu Dogara Ya Fara Samun Tabuwan Hankali Hoto: YIAGA Africa
Asali: Twitter

Sanarwar da kwamitin ya fitar tace

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Da alamu tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya yanke ƙauna tunda burinsa na neman tikitin takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC bai cika ba.
A kan haka ne ya zama mai tada zaune tsaye, yana jefan mu da kalaman kiyayya da adawa, da nufin ɗagawa kasarmu hankali kan wannan batun.
“Don haka kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Tinubu/Shettima bai yi mamakin yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka rika yaɗa wani taro na wasu da ake kira shugabannin Kiristocin Arewa, wadanda suka yi ikirarin cewa su ‘ya’yan jam’iyyarmu ta APC ne kuma suke sukar mu da ire-iren waɗannan batutuwa"

APC ta yiwa ɗan takarar shugaban kasa na PDP shaguɓe, tace baya Fatakwal baya London.

A wani labarin kuwa, kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, ta caccaki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

Wannan dai na ƙunshi ne cikin sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ya fitar Bayo Onanagu, yace

"Duk ƴan Najeriya suna sane da cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP Atiku ya yi ƙaurin suna wajen ƙarya da kuma ƙarya ka’idar karba-karba tsakanin arewa da kudu. Dagewar da ya yi na kwace iko da jam'iyyar ya sa ya haifar da rikici a cikin jam’iyyarsa, wanda kuma hakan ya sa ya kasa tsayawa, baya Fatakwal baya London"

Asali: Legit.ng

Online view pixel