APC Ta Kaddamar da Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Mata

APC Ta Kaddamar da Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Mata

  • A yau Litinin 10 ga watan Oktoba ne jam'iyyar APC ta kaddamar da majalisar kamfen dinta na mata a babban birnin tarayya Abuja
  • Manyan jiga-jigan APC sun taru domin kaddamar da matan da za su tallata dan takarar shugaban kasa Bola Tinubu
  • INEC ta amincewa jam'iyyun siyasa a Najeriya su fara kamfen gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa

FCT, Abuja - An kaddamar da sashen mata na tawagar kamfen din Tinubu na jam'iyyar APC gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

A halin yanzu ne ake gudanar da kaddamarwar a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja, uma manyan jiga-jigan APC ne suka samu halarta, ciki har da shugaba Buhari.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ma ya samu halarta, inji rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

APC ta kaddamar da majalisar kamfen din Tinubu na mata
APC Ta Kaddamar da Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Mata | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito wadanda suka halarci taron sun hada da:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

  1. Dan takarar shugaban kasna APC, Asiwaju Bola Tinubu
  2. Mataimakin Tinubu, Sanata Kashim Shettima
  3. Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu
  4. Uwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari
  5. Mata Tinubu, Sanata Remi Tinubi
  6. Matar Shettima, Misis Nana Shettima
  7. Shugaban gwamnonin APC, gwmna Simon Lalibg
  8. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo
  9. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano
  10. Ministar mata Pauline Tallen
  11. Shugaban mata ta APC na kasa, Beta Edu
  12. Da sauran kusoshin jam'iyyar APC

Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga

A wani labarin na daban, bincike ya nuna cewa, kasafin kudin 2023 da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a makon jiya ya bayyana adadin kudaden da ofishinsa da na mataimakinsa za su ci a fannin tafiya da abinci kadai ya zarce N11.92bn a shekarar.

Kara karanta wannan

Ba Zai Yuwu Mu sha Kaye a 2023: Aisha Buhari Tayi Muhimmiyar Ganawa da Matar Tinubu

Tafiye-tafiyen da ake nufi anan na cikin gida ne da wajen kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Punch a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba ta bayyana cewa, an ware N1.58bn domin kula da lafiyar jiragen sama, yayin da aka ware N1.60bn domin gyara injunan jiragen Gulfstream GV da CL605.

Asali: Legit.ng

Online view pixel