Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

  • Hajiya Aisha Buhari, mai dakin shugaban Najeriya ta roki afuwan yan Najeriya kan rashin tsaro
  • Mai dakin shugaba Muhammadu Buharin ta ce rage darajar naira da kuma faduwar darajar naira a kasuwancin canji ya jefa yan kasa cikin mawuyacin hali
  • Aisha ta kuma jinjinawa dakarun tsaro na kasar bisa gudunmawa da suka bayarwa wurin yaki da rashin tsaro ta kuma musu fatan alheri

FCT Abuja - Mai dakin shugaban kasa, Hajia Aisha Muhammadu Buhari, ta bawa yan Najeriya hakuri kan rashin tsaro da tsadar rayuwa da ya jefa yan kasar cikin rayuwar kunci a shekaru bakwai da suka shude.

Ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin addu'a da lakca ta musamman don bikin ranar samun yancin kai karo na 62 da aka yi a masallacin kasa a Abuja, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Aisha Buhari.
Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa. Hoto: @NigerianTribune.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ta, rage darajar naira da cigaba da faduwar darajar naira a kasuwannin canji ya shafi tattalin arziki wacce ta ce ya yi sanadin wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta wurin ilimi, lafiya da harkokin yau da kulum.

Duk da haka ta yaba wa kokarin dakarun sojoji wurin magance kallubalen tsaro a kasar kuma ta musu fatan alheri.

Wani sashi cikin jawabin ta:

"Kamar yadda kuka sani, wani gwamnatin tana dafa da zuwa karshen wa'adinta kuma wanna shine bikin yancin kai na karshe da za ta yi, ina addu'ar mu yi zabe lafiya da mika mulki.
"Ba dole ne gwamnatin ta zama ba ta da nakasu ba, amma ina son yin amfani da wannan damar in nemi yafiya daga yan malamai da yan Najeriya baki daya. Akwai bukatar dukkan mu muyi aiki tare don bunkasa Najeriya."

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

Ta cigaba da cewa:

"Na yi murnar gani cewa jami'an tsaron mu sun tashi suna tunkarar kallubalen fiye da kowane lokaci. A wannan lokacin a baya. A yanzu suna kokarin kawo karshen yan bindiga, masu garkuwa da sauran bata gari. Ina jinjinawa kokarin jarumar jami'an tsaron mu kuma ina addu'a Allah ya kara musu nasara."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel