Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40

Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40

  • Allah ya yiwa wata matar aure rasuwa bayan ta haifo kyawawan yaranta guda uku a wani sansanin yan gudun hijira da ke jihar Borno
  • Sai dai kuma yaran sun zama cikakkun marayu domin mahaifinsu ma ya kwanta dama kwanaki 40 bayan rasuwar mahaifiyar tasu
  • Wannan al'amari ya taba zuciyar dan marigayi tsohon ministan Najeriya kuma dan siyasar Borno, Shettima Ali Monguno

Borno - Wata matar aure ta rasu bayan haihuwar yan uku a sansanin yan gudun hijira da ke jihar Borno.

Rahma Monguno, dan marigayi tsohon ministan Najeriya kuma dan siyasar Borno, Shettima Ali Monguno, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, ya ce mijin matar ya bita bayan kwanaki 40 da rasuwarta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da bam ya tashi bayan sallar Juma'a, mutane da dama sun mutu

Yan uku
Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40 Hoto: Rahma Monguno, Fiona Lovatt
Asali: Facebook

Ya rubuta a shafinsa na Facebook:

“Daya daga cikin labara mai taba zuciya da na taba yin karo da shi, a jiyan nan mun je wani sansani don ganin wasu zawara, mun yi tafiyar ne ga wani makusanci da ke son taimakawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yan ukun sun rasa mahaifiyarsu a wajen haihuwarsu, mahaifin ya rasu shina bayan kwanaki 40 (Allah ya ji kansu da rahama).
“Yar’uwar mahaifiyarsu da diyarta wacce itama bazawara ce sune suke kula da su.
“Allah madaukakin sarki ya saka masu da alkhairi ya kuma albarkaci duk wadanda ke sa hannu a lamarin, sannan ya baiwa iyalin makoma fiye da tsammaninsu.”

Jama'a sun yi martani

Abubakar Mohammed ya rubuta:

"Masha Allah. Allah ya albarkaci rayuwa."

Adam Kambarima ya yi martani:

"Masha Allah."

Maryam Abdullahi Jidayi

"Allah ya albarkace ka."

Ahmed Zanna Mohammed ya rubuta:

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

"ALLAH SARKI."

Swabr Ventures ya yi martani:

"Aameen Yaa Allaah, Yaa ArhamarRaahimeen."

Sarkin Argungu Ya Gabatar Da Wani Babban Bukata A Gaban Gwamnatin Birtaniya

A wani labari na daban, mai martaba sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera ya roki gwamnatin Birtaniya da ta taimaka ta dawo da wasu daga cikin kayayyakin tarihi na masarautar Kabi da aka tafi da su a lokacin mulkin mallaka.

Basaraken ya yi wannan rokon ne lokacin da ya karbi bakuncin babbar kwamishinar Birtaniya a Najeriya, Cantriona Laing a fadarsa da ke Argungu, jaridar The Nation ta rahoto.

Sarkin ya yi bayanin cewa wasu daga cikin tsoffin kayan tarihin sun bata ne a lokacin mulkin mallaka a masarautar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel