Dole Ka Tattara Komatsanka Ka Koma Najeriya: 'Yar Amurka Da Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta, Bidiyon Ya Yadu

Dole Ka Tattara Komatsanka Ka Koma Najeriya: 'Yar Amurka Da Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata fusatacciyar mata yar Amurka ta sha alwashin yin maganin mijinta dan Najeriya wanda ta kama yana cin amanarta da wata budurwarsa
  • A wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo, matar ta sanar da mijinta kai tsaye cewa kada ya kuskura ya kara taka kafarsa a gidanta
  • Matar wacce ta matukar tunzura ta kuma ce mutumin zai koma Najeriya yayin da take zagin budurwar tasa

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun sha mamaki da ganin wani bidiyon wata Ba’amurkiya tana yiwa mijinta dan Najeriya wankin babban bargo a bainar jama’a.

Matar mai suna Shamika Moore a TikTok, ta fusata bayan ta gano cewa mijinta na soyayya da wata mace.

Saurayi da budurwa
Dole Ka Tattara Komatsanka Ka Koma Najeriya: 'Yar Amurka Da Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@shamikamoore4.
Asali: UGC

Wani bidiyon TikTok ya nuno lokacin da Shamika ta kama mijinta da budurwar, kuma ta kasa shanye halin bakin ciki da ta shiga.

Nan take ta zazzagesu su dukka biyun yayin da suke a cikin wata mota. Ta fada ma mutumin cewa zai koma Najeriya, tana mai gargadinsa da kada ya dawo gidanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwar ta rama zagin, tana mai fada ma matar cewa mutumin ba zai dawo gareta ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@ja.x.licreates ta yi martani:

“Yarinya! Da na yaga gaba daya kofar.”

@Crystal L Pen ta yi martani:

“Ki barta ta mallake shi. Saboda itama haka zai yi mata.”

@LadyLove10 ta ce:

“Yarinya gwanda tayiwa kanta fada, saboda lamarin na juyawa garesu cikin sauri.”

Labaarin Wani Dan Saudiyya Ya Yi Ikirarin Cewa Ya Yi Aure Sau 53 a Cikin Shekaru 43

A wani labarin, mun ji cewa a kokarinsa na neman kwanciyar hankali da dadin rai, wani balarabe ya fadi tarihin rayuwarsa, ya ce mata 53 ya aura a cikin shekaru 43 kacal.

Abu Abdullah ya ce ya yi aurensa na farko ne a lokacin yana da shekaru 20, kuma matar da ya aura ta girme shi da shekaru shida.

An kakaba masa “Polygamist of the century”, wato mutumin da ya fi yawan aure-aure a wannan kanin saboda yawan auren da ya yi, kamar yadda MBC ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel