Gwamnatun Najeriya Ta Ce Cin Fatan Dabbobi Bai da Wani Amfani, Za a Haramtawa ’Yan Najeriya

Gwamnatun Najeriya Ta Ce Cin Fatan Dabbobi Bai da Wani Amfani, Za a Haramtawa ’Yan Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya na shirin kawo dokar da za ta haramtawa 'yan Najeriya cin fatan dabbobi saboda wasu dalilai
  • Daraktan cibiyar NILEST ya bayyana cewa, kwata-kwata cin fatan dabbobi bai da wani amfani a jin dan adam
  • A baya an sha muhawara a majalisar dokokin Najeriya don duba yiwuwar samar da dokar da zata haramta cin fatu

Zaria, Kaduna - Gwamnatin Najeriya na shirin kawo kudirin dokar da zai haramta cin fatar dabbobi da aka fi sani Ponmo a kasar saboda habaka masana'antun fata.

Muhammad Yakubu, babban daraktan cibiyar fata da kimiyya ta NILEST dake Zaria ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, TheCable ta ruwaito.

Za a haramta acin fatan dabbobi a Najeriya
Gwamnatun Najeriya Ta Ce Cin Fatan Dabbobi Bai da Wani Amfani, Za a Haramtawa ’Yan Najeriya | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yakubu ya ce wannan yunkuri ya zama dole domin farfaɗo da masana'antun fata a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Ya kuma bayyana cewa, cibiyar da yake kula da ita da kuma sauran masana'antun fata za su tunkari majalisar dokokin kasar da na jihohi don tabbatar da haramcin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"A iya sani na, 'yan Najeriya ne kadai mutanen da a duniya suke rage darajar fata ta hanyar mai da ita abinci, duk da cewa Ponmo bai da wani amfani a jiki.
"A wani lokaci, an taɓa kai batun gaban majalisun biyu na dokokin kasar nan, kuma an yi muhawara a kai, amma ban san me shashashantar da batun ba."

Dalilin koma baya a masana'antun fata

A fahimtarsa, yawan cin fatan dabbobi a Najeriya na daga cikin dalilan da suka kawo koma-baya a fannin masana'antun fata.

Ya kuma bayyana cewa, duk da haka dokar kasa a fannin fata ta kawo wasu sauye-sauyen da suka rage matsalolin da fannin ke fuskanta, haka nan People's Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

A kalamansa:

"Idan muka inganta masana'antun fatunmu, kuma kuma ana samar da takalma da sauran kayan fata a Najeriya, zai ba jama'a wahala su samu fata balle ma su iya ci.
"Idan aka tabbatar da dokar gaba daya, zata sauya durkusassun masana'antun fatu da dama sannan a samu sakamako mai gwabi."

Yakubu ya kuma kirayi masu ruwa da tsaki da su goyi bayan wannan kudirin a majalisa sannan su tabbatar da yiwa dokar kasa kan fantu kwaskwasrima.

An kafa cibiyar NILEST ne don habaka masana'antun fata a karkashin Dokar Cibiyar Binciken Harkar Noma, 1975.

Cibiyar na gudanar da bincike kan sarrafawa da samar da fatu da kayayyakin fannin a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kawar da Amfani da Kananzir Nan da Shekarar 2023

A wani labarin, domin magancewa da samar da mafita ga matsalolin da suka shafi sauyin yanayi, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar haramta amfani kananzir nan da shekarar 2030, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Hakazalika, ta kuwa yanke shawarar kawar da gurbatattun kayayyaki a fannin man fetur da iskar gas nan da shekarar ta 2030.

Wannan na fitowa ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, a wajen bude taron hada-hadar kudi karo na 15 da cibiyar ‘Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) ta shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel