Bidiyo: Yadda Yar Najeriya Mazauniyar UK Ta Fatattaki Mijinta Daga Gida Saboda Ya Kira Mata Yan Sanda

Bidiyo: Yadda Yar Najeriya Mazauniyar UK Ta Fatattaki Mijinta Daga Gida Saboda Ya Kira Mata Yan Sanda

  • Wata matashiya yar Najeriya da ke zaune a UK ta fatattaki mijinta bayan ya kira mata yan sanda
  • An tattaro cewa mijinta ya sako yan sanda a lamarinsu bayan ta yi barazanar kashe shi da wani makami a yayin da suka samu sabani
  • An rahoto cewa mutumin ne ya kai matar UK sannan ya dauki nauyin karatunta na jami’a a kokarinsa na ganin ta samu aiki mai kyau

UK - Matar wani dan Najeriya mazaunin UK mai suna Charles ta fatattake shi daga gida inda ta watsa masa kayansa waje.

Shafin Instablog9ja wanda ya wallafa bidiyoyin lamarin, ya rahoto cewa mutumin ya kira yan sanda bayan matarsa ta yi barazanar kashe shi da wani makami yayin da suke musayar yawu.

Mata da miji
Bidiyo: Yadda Yar Najeriya Mazauniyar UK Ta Fatattaki Mijinta Daga Gida Saboda Ya Kira Mata Yan Sanda Hoto: @instablog9ja
Asali: UGC

Shafin ya ce wata majiya ta bayyana cewa mutumin ne ya kai matashiyar UK sannan ya dauki nauyin karatunta duk don ta samu aiki mai kyau domin suna da yara tare.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Za ta Kirkiro Bankuna na Musamman Domin Matasan Najeriya

Majiyar ta yi ikirarin cewa ta fusata ne kan shawarar da mijinta ya yanke na sako yan sanda a lamarin, inda hakan yasa ta kore shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai da mijin nata ya sako abokansa cikin lamarin yayin da ya tattara kayayyakinsa. A cewar majiya, matar ta yiwa abokan mijin da makwabtansu rashin mutunci.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@casie_udeg_ ta yi martani:

“Auren yan Najeriya a kasar waje ba na ragon mutum bane…Kashe kudi na sa kowa ya zauce da daukar mataki.”

@organicoilplus ta ce:

“Bana yarda da labarin bangare daya dan Allah, idan kana sauraron Igbo z aka fahimta…wasu mazan sun iya zautar da mace sannan suyi kamar basu ne da laifi ba idan ta dauki mataki.”

@myselfdefense_ng ya ce:

“Wannan abun bakin ciki ne kuma babu wanda ya cancanci shiga wannan hali da ace a Najeriya ne da iyayensu sun sulhunta su.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta

Sai Da Aka Kwabe Ni: Wata Budurwa Ta Bayyana Alhininta Na Kulla Soyayya Da Dan Najeriya

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar kasar Kenya mai suna, Huddah Monroe, ta nuna nadamarta na kin bin maganar mahaifiyarta da goggwaninta.

Monroe ta ce mahaifan nata sun kwabeta a kan soyayya da mazan Afrika ta yamma musamman ma mazan Najeriya amma ta ki ji.

Shafin LIB ya rahoto cewa budurwar ta bayyana hakan ne yayin da take tuna lokacin da shugaban kasar Kenya, William Ruto ya yarda cewa mawuyacin abu ne gare shi aurar da diyarsa ga dan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel