An Je Kotu, Rashin Lafiya Ya Kama Lauyan da Ya Shigar da Kara a Hana Atiku Takara

An Je Kotu, Rashin Lafiya Ya Kama Lauyan da Ya Shigar da Kara a Hana Atiku Takara

  • Prince Michael Ekamon ya koma kotu da Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal a madadin Nyesom Wike
  • Amma Lauyan da ya tsayawa Ekamon,Wilfred Okoai bai samu zama a wannan shari’a da ake yi a Abuja ba
  • An fadawa Alkali cewa ciwon ciki ya murde Lauyan, wannan ya sa dole ya bar kotu domin ya nemi magani

Abuja - Prince Michael Ekamon wanda suka shigar da karar Atiku Abubakar ya fadawa kotu cewa Lauyansu, Wilfred Okoi yana fama da rashin lafiya.

Vanguard ta rahoto Prince Michael Ekamon yana cewa Wilfred Okoi bai samu zuwa kotu yau ba saboda larurar rashin lafiya domin cikinsa ya murde.

Masu shigar da kara sun sanar da Alkali Ahmed Mohammed na babban kotun tarayya na Abuja cewa lauyan ya zo kotun, amma ciki ya sa shi gaba.

Kara karanta wannan

Harin 9/11 Na Amurka: Fasto Adebayo Ya Bayyana Yadda Aka Bincike Shi Saboda Yunkurin Siyan Jirgi

A sakamakon haka, dole Wilfred Okoi ya bar kotun domin ya kula da ciwon da ke damunsa.

Okoi ya rubuta sunansa a wadanda suka halarci kotun, amma da za a fara shari’a, sai aka neme shi aka rasa, Alkali yace babu bukatar a binciki maganar.

Okoi ya zo kotu da safen nan, sai ya yi kukan cikinsa yana murdawa, dole aka ruga da shi domin a nema masa maganin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku
Atiku Abubakar Hoto: PDP
Asali: UGC

Na nemi Okoi ya tsaya, amma sai ya dage cewa mu kai shi inda zai samu magani.

Alkali ya ji tausayin Lauya

Alkali ya yi wa Lauyan addu’ar samun lafiya da gaggawa, ya kuma ce babu wani ‘Dan Adam da ya fi karfin ciwo ya fado masa a kowane irin lokaci.

P/Times tace Ekamon ya roki a kara masa lokaci tun da wanda yake kare shi bai iya zuwa kotun ba, Mai shari’an ya amince da wannan bukatar.

Kara karanta wannan

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Fitaccen Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

Lauyoyi sun gamsu

Lauyan Aminu Tambuwal wanda shi ne mai ba jam’iyyar PDP shawara a harkar shari’a bai nuna rashin amincewarsa kan bukatar da aka kawo ba.

Shi ma Lauyan Atiku Abubakar, Mahmud Magaji SAN ya ya yarda a karawa Lauyan na Ekamon lokaci. Sai nan da 7 ga watan Oktoba za a koma kotun.

Abin da ya sa mu ka je kou - Lauya

Ku na da labari Prince Michael Ekamon ya fadawa kotu suna kalubalantar tsaida Atiku Abubakar da PDP tayi a matsayin ‘dan takarar a zaben 2023.

Ekamakon ya shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/22 a watan Yuni. Shi Nyesom Wike wanda ake karar saboda shi yace babu ruwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel