Wani Matashi Dan Shekara 17 Ya Nutse A Kududufi A Jihar Kano

Wani Matashi Dan Shekara 17 Ya Nutse A Kududufi A Jihar Kano

  • Allah ya yi wa wani matashi Suleiman Muhammad dan shekara 17 rasuwa a Wailari Quaters, Kano
  • Marigayin ya rasu ne sakamakon wanka da ya tafi yi a wani kududufi da ke unguwarsu a ranar Talata
  • Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kwana-kwana na Kano ya ce mutanensu sun isa wurin da abin ya faru sun ciro shi a sume daga bisani aka tabbatar ya rasu

Kano - Wani matashi dan shekara 17, Suleiman Muhammad, ya nutse a wani kududufi da ke Wailari Quaters a karamar hukumar Kumbotso na Jihar Kano.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na Jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a Kano, Premium Times ta rahoto.

Kududufi
Wani Matashi Ya Nutse A Kududufi A Kano. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Mr Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Ta Gana Da ASUU, Ta Bukaci Su Janye Yajin Aiki A Jami'o'in Jihar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Mun samu kiran neman dauki na gaggawa misalin karfe 3.47 daga wani Muhammad Salisu kuma muka aika tawagar mu na ceto zuwa wurin suka isa misalin karfe 3.57 na rana.
"An ciro Muhammad daga cikin kududufin a sume kuma daga bisani aka tabbatar ya riga mu gidan gaskiya."

Mr Abdullahi ya ce an mika wa dagacin Wailari Quaters, Magaji Adamu, gawar matashin.

Ya ce sanadin rasuwar shine 'wanka a kududufin' da marigayin ya tafi yi kamar yadda NAN ta rahoto.

Yadda Wani Mutumin Jigawa Ya Nutse Garin Ceto Shanunsa A Kududufi

A wani rahoton, wani matashi dan shekara 18, Adamu Musa na Unguwar Magina, a garin Buji, karamar hukumar Buji na Jihar Jigawa ya rasu a kududufi yayin kokarin ceto shanunsu wacce ta zame ta fada kududufin yayin kiwo.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Shekara 55 Da Ya Lalaba Cikin Dare Ya Saci Plantain Na N4,000 Daga Gonar Wani A Ibadan

Kakakin rundunar tsaro ta NSCDC na Jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce abin bakin cikin ya faru ne a ranar Asabar misalin karfe 2 na rana lokacin da matashin ya kai shanunsa biyu gona ya sake su suyi kiwo a kusa da gonar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel