Yadda Wani Mutumin Jigawa Ya Nutse Garin Ceto Shanunsa A Kududufi

Yadda Wani Mutumin Jigawa Ya Nutse Garin Ceto Shanunsa A Kududufi

  • Adamu Musa, wani matashi mai shekara 18 mazaunin unguwar Magina a Buji, karamar hukumar Buji ya mutu wurin ceto shanunsa
  • Rahotanni sun bayyana cewa shanun ta zame ta fada kududufi ne yayin da ta ke kiwo shi kuma Musa ba shiga kududufin ya ceto ta amma shi ya nutse
  • Mutanen gari da jami'an hukumar NSCDC sun yi kokarin ceto Musa amma ba su yi nasara ba sai bayan kimanin awa 24 aka gano gawarsa

Jigawa - Wani matashi dan shekara 18, Adamu Musa na Unguwar Magina, a garin Buji, karamar hukumar Buji na Jihar Jigawa ya rasu a kududufi yayin kokarin ceto shanunsu wacce ta zame ta fada kududufin yayin kiwo.

Kakakin rundunar tsaro ta NSCDC na Jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Akan N1,500 na kudin wutan lantarki, wani ya bindige kaninsa har lahira

Shanu
Yadda Wani Mutumin Jigawa Ya Nutse Garin Ceto Shanunsa A Kududufi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce abin bakin cikin ya faru ne a ranar Asabar misalin karfe 2 na rana lokacin da matashin ya kai shanunsa biyu gona ya sake su suyi kiwo a kusa da gonar.

Ya ce, abin bakin ciki, daya cikin shanun ta zame ta fada cikin kududufi da ke kusa da gonar yayin da suke kiwo.

Kakakin hukumar ya ce, ganin abin ya faru, Musa ya garzaya don ceto shanunsa, amma ya nutse, duk da kokarin da mutanen yankin da NSCDC suka yi don ceto shi, ba a gano shi ba sai karfe 1 na yau Lahadi.

Shehu ya ce:

"An duba shi sosai, sannan aka tabbatar ya rasu kuma aka mika wa iyayensa gawar domin yi masa jana'iza yayin da ita kuma shanun an ceto ta ta rai."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel