An Kama Matashi Hassan Kan Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 90 Don Ya Sace Katin ATM Dinsa Na Banki

An Kama Matashi Hassan Kan Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 90 Don Ya Sace Katin ATM Dinsa Na Banki

  • Jami'an yan sanda sun kama wani Hassan Ibrahim kan zarginsa da halaka mahaifinsa, Sabi Ibrahim dan shekara 90 a Kwara
  • Bayan yan sanda sun kama shi, Hassan ya amsa cewa ya yi wa mahaifinsa allura da yasa jikinsa ya mutu sannan ya kai shi wani kango ya halaka shi ya birne shi
  • Kakakin yan sandan Jihar Kwara Ajayi Okasanmi ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin

Kwara - Yan sanda a Jihar Kwara sun kama wani Hassan Ibrahim kan kashe mahaifinsa dan shekara 90, Sabi Ibrahim, don karbe katinsa na ATM na cire kudi a banki, Vanguard ta rahoto.

Kakakin yan sandan Jihar, SP Ajayi Okasanmi ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Ilorin yana cewa wata Aisha Ibrahim ne ta kai wa yan sanda rohoton a ranar 5 ga watan Agusta cewa Sabi ya bace.

Kara karanta wannan

Alkali Ya Tura Dan Sufetan Yan Sanda Gidan Yari Kan Satar Motar N52m A Legas

Matashi
Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Mai Shekara 90 Don Ya Sace Katin ATM Dinsa Na Banki. @VanguardNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa bata tsohon da tsohon sojan mai shekara 90 da ya yi ya bada mamaki.

Okasanmi ya ce:

"Binciken da aka yi kan lamarin ya yi sanadin kama Hassan, dan dattijon da ya bace.
"Yayin bincike, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya yi wa mahaifinsa allurar sinadarin maganin ciwon jiki da wasu abubuwan, nan take jikinsa ya mutu kuma ya fara ganin jiri.
"Ya aikata hakan ne bayan sun dawo daga banki tare da mahaifin nasa ya karbo katin ATM na cire kudi."

Ya cigaba da cewa:

"Daga nan ya karbo aron babur ya dauki mahaifinsa ya kai shi wani kangon gini ya shake shi har sai da ya rasu sannan ya dauki katinsa na ATM.
"Daga nan ya haka rami mara zurfi ya binne mahaifinsa bayan ya raba shi da katinsa na ATM."

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Koma Makarantar Da Nayi Digiri Nace Su Dawo Min Da Kudi Na

Hassan ya tsere Kaduna ya fara cire kudaden mahaifinsa - Okasanmi

Kakakin yan sandan ya kara da cewa bayan hakan ne Hassan ya tsere Jihar Kaduna ya fara cire kudi daga asusun ajiyar banki na mahaifinsa. Ya fara cire N59,000 kafin aka kama shi, rahoton Punch.

Okasanmi ya kuma ce Hassan ya sayar da babur din da ya aro kafin ya tsere Kaduna inda aka kama shi.

Ya ce:

"An karbo katin na ATM da babur din da ya sace."

Za a gurfanar da Hassan a gaban kotu bayan an kammala bincike, kakakin yan sandan ya bada tabbaci.

Damfara Ta N26.7m: Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Maka Mataimakin Kwamandan NSCDC a Kotu

A wani rahoton, Hukumar ICPC ta yi karar wani mataimakin kwamanda na hukumar tsaro ta NSCDC, Edike Mboutidem Akpan a wata babban kotun tarayya a Abuja kan zarginsa da amfani da kamfanin dillancin gidaje/filaye, Danemy Nig Ltd, don damfarar kwastomomi kudi har N26,655,000.

Mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel