Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila, Ya Saki Jawabinsa Na Farko

Yarima Charles, Ya Zama Sabon Sarkin Ingila, Ya Saki Jawabinsa Na Farko

Biyo Bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth, Yariman Charles, ya zama Sarkin Masarautar Ingila, Fadar Mulkin Buckingham ta sanar ranar Alhamis.

Charles mai shekaru 73 ne babban 'dan Elizabeth.

Sauran 'yayanta sun hada da Gimbiya Anne, 72, Yarima Andrew, 62, da Yarima Edward, 58.

Gabanin mutuwarta dukkansu suka garzaya Balmoral don zaman karshe da ita.

A jawabinsa na farko matsayin Sarki, Charles ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa da kuma yadda suke jimami.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Legit.ng

Online view pixel